Yanzu-yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano ya koma APC

Yanzu-yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano ya koma APC

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, wanda yayi murabus a kwanakin baya ya koma jam'iyyar All Progressive Party (APC) bayan komawa jam'iyyar adawa ta PDP da kuma PRP.

Mai magana da yawun farfesa Hafiz Abubakar, AbdulWahab Sa'id ya ce maigidansa ya koma APC ne bayan wata ganawa da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a daren Laraba tare da wasu abokan siyasan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

AbdulWahab wanda ya tabbatar da wannan labari a ranan Alhamis bai yi bayani kan abubuwan da suka tattauna akai amma yace akwai wasu shirye-shirye da sukeyi kan sauya shekar.

KU KARANTA: Gudaji Kazaure ya kwancewa 'yan PDP zani a kasuwa kan Buhari

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wata tawaga daga jihar Kano wanda ya kunshi tsohon mataimakin gwamnan jihar, Hafiz Abubakar; tsohon ma'ajin jam'iyyar APC, Bala Gwagwarwa da tsohon shugaban hukumar NPA, Aminu Dabo, Injinya Mu'azu Magaji da Sanata Isa Zarewa.

Babban hadimin gwamnan jihar Kano, Salihu Tanko Yakassai ya raba wannan labari da jaridar Solacebase ta tabbatar.

Jaridar ta tattaro cewa bayan ganawarsu da Buhari, tawagan wacce gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya jagoranta sun nuna niyyar komawa jam'iyyar APC da kuma taimakawa nasarar jam'iyyar

A kwanakin nan, kungiyar Kwankwasiyya na fuskantar kalubale yayinda manya-manyan jigoginta na fita suna hada kai da gwamnan jihar. Tsohon kwamishana a gwamnatin Kwankwaso, Janar Idris Bello Dambazzau da Balaraba Ibrahim sun kona APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel