2019: Amfani da jami'an soji wajen murdiyar zabe zai haddasa tashin hankali - Ezekwesili

2019: Amfani da jami'an soji wajen murdiyar zabe zai haddasa tashin hankali - Ezekwesili

- Dr Obiageli Ezekwesili, ta yi gargadin cewa amfani da jami'an soji dama sauran jami'an tsaro wajen murdiyar zaben 2019 zai iya jefa kasar cikin tashin hankali

- Ta bayyana kokontonta kan yiyuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari na tabbatar da yin adalci da wanzar da zaman lafiya a zaben mai zuwa

- Tawagar wakilan cibiyoyin IRI da NDI sun iso Nigeria tun a ranar 14 ga watan Disamba don ganawa da manyan masu ruwa da tsaki a harkokin gudanar zabe

Yar takarar shugabar kasa karkashin jam'iyyar ACPN, Dr Obiageli Ezekwesili, ta yi gargadin cewa amfani da jami'an soji dama sauran jami'an tsaro wajen murdiyar zaben 2019 zai iya jefa kasar cikin tashin hankali.

Ta bayyana kokontonta kan yiyuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari na tabbatar da yin adalci da wanzar da zaman lafiya a zaben mai zuwa.

A cikin wata sanarwa daga kungiyar yakin zabenta a daren ranar Laraba, ta ce Ezekwesili ta bayyana hakan a wani taro da cibiyar harkokin jama'a ta kasa da kasa IRI da kuma cibiyar demokaradiyya ta kasa da kasa NDI, kan nazarin zaben 2019.

KARANTA WANNAN: Disamba 22: Real Madrid zata san makomarta a gasar zakarun nahiyoyi

2019: Amfani da jami'an soji wajen murdiyar zabe zai haddasa tashin hankali - Ezekwesili
2019: Amfani da jami'an soji wajen murdiyar zabe zai haddasa tashin hankali - Ezekwesili
Asali: Twitter

Ta ce, "Ya zama wajibi shugaban kasa Buhari ya tashi tsaye wajen magance rikicin da kasar zata iya shiga ma damar aka ce za a yi amfani da jami'an soji da na 'yan sanda wajen murdiyar zabe, wanda kuma hakan kutse ne ga demokaradiyya, la'akari da zaben jihohin Osun da Eikti.

"Ya zama wajibi a tsame dukkanin wasu jami'an tsaro daga harkokin zabe, kamar yadda aka samu rikici a zabukan gwamnonin jihohin biyu. Nigeria na bukatar sabuwar turba, kuma ya zama wajibi shugaban kasar ya kaucewa duk wasu abubuwa da ka iya jawo rikici tsakanin al'ummar kasar a zaben 2019.

"Duk wani yunkuri da shugaban kasar zai yi don samawa kansa tagomashi a zaben watan Fabrerun 2019, zamu kalle shi a matsayin cin hanci da rashawa na siyasa, tunda yana amfani da karfin ikon mulki ne wajen ganin ya samu nasarar takarar da yake yi," a cewar Ezekwesili.

Tawagar wakilan cibiyoyin IRI da NDI sun iso Nigeria tun a ranar 14 ga watan Disamba don ganawa da manyan masu ruwa da tsaki a harkokin gudanar zabe, don ganin an gudanar a sahihin zaben 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel