Disamba 22: Real Madrid zata san makomarta a gasar zakarun nahiyoyi

Disamba 22: Real Madrid zata san makomarta a gasar zakarun nahiyoyi

- Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata san makomarta a gasar zakarun nahiyoyi a ranar Asabar, 22 ga watan Disambar 2018

- Real Madrid ta lallasa kungiyar Kashima Atlers ta kasar Japan da kwallaye 3-1 a wasan na kusa dana karshe

- A ranar Asabar, Madrid zata kara da kungiyar Al Ain ta kasar hadaddiyar Daular Larabawa, don buga wasan karshe na gasar zakarun nahiyoyin

Bayan gagarumar nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu na kaiwa wasan zagayen karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyoyin duniya, sakamakon lallasa kungiyar kwallon kafa ta Kashima Atlers ta kasar Japan da kwallye 3-1; a ranar Asabar ne zata san makomarta a gasar.

A yayin wasan nata da Kashima Atlers, dan wasan gaba na Real Madrid, Gareth Bale, shine ya jefa duka kwallaye 3 a cikin ragar abokan karawar tasu, kuma wasan ne ya kasance na kusa dana karshe a gasar, wanda aka buga a filin wasanni na Abu Dhabi.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Rundunar sojin Nigeria ta fara daukar sabbin ma'aikata

Disamba 22: Real Madrid zata san makomarta a gasar zakarun nahiyoyi

Disamba 22: Real Madrid zata san makomarta a gasar zakarun nahiyoyi
Source: Getty Images

Sai dai duk da wannan nasarar da Real Madrid ta samu, akwai babban kalubale a gabanta a ranar Asabar, inda zata buga wasan karshe da kungiyar Al Ain ta kasar Daular Larabawa, wacce itama ta samu nasarar lallasa kungiyar River Plate ta Agentina.

Samun nasara ga Real Madrid a wasan na ranar Asabar, zai bata damar lashe kofin duniyar na zakarun kungiyoyin nahiyoyi sau uku a jere.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel