Da dumi dumi: Rundunar sojin Nigeria ta fara daukar sabbin ma'aikata

Da dumi dumi: Rundunar sojin Nigeria ta fara daukar sabbin ma'aikata

Rundunar sojin Nigeria ta sanar da fara dibar sabbin dakaru, ga masu sha'awar shiga aikin sojin kasar. Bayanin hakanna kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Laraba, inda ta ce dukkanin masu sha'awa na iya cikewa a tsarin 'trades/non-trades' na bangaren maza da mata.

A ranar Laraba, rundunar sojin Nigeria ta fitar da sanarwar fara daukar sabbin dakarun soji, wadanda zasu yi aiki karkashin tsarin 'tardes/non-trades', da aka ware don amza da mata.

Rundunar ta bude kofar fara dibar sabbin ma'aikatan ne a ranar 19 ga watan Disamba, inda kuma zata kulle karbar bukatun masu sha'awar shiga akin a ranar 31 ga watan Janairu, 2019.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Kungiyoyin siyasa 469 za su bar tafiyar Atiku ma damar ba a wai waye su ba

Da dumi dumi: Rundunar sojin Nigeria ta fara daukar sabbin ma'aikata

Da dumi dumi: Rundunar sojin Nigeria ta fara daukar sabbin ma'aikata
Source: UGC

A yayin da rundunar sojin ta jaddada cewa karbar form da cikewa kyauta ne, ta kuma cewa dukkanin masu shja'awar shiga aikin sojin, dole su kasance masu shekaru tsakanin 18 zuwa 22, kuma zasu iya cike bayansu a shafin rundunar na yanar gizo, recruitment. army.mil.ng

"Muna sanar da daukacin jama'a, cewar shafin daukar ma'aikatanmu na yanar gizo na 78RRI a matakin 'trades/non-trades' ga mata da maza, zai kasance a bude don bada dama ga masu sha'awar shiga aikin soji," a cewar rundunar sojin a ranar Laraba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel