Kotu ta jefa Lebura kurkuku kan laifi satan cebur da diga

Kotu ta jefa Lebura kurkuku kan laifi satan cebur da diga

Wata kotun majistaren jihar Sokoto a ranan Talata ya yankewa wani matashin lebura masi suna, Anas Muhammad, hukuncin watanni bakwai a gidan yari kan laifin satan drum 2, diga da cebur na makwabta.

Alkalin majistaren, Abubakar Adamu, ya aika Muhammad kurkuku kuma ya hanashi beli bayan ya amince da laifin da ake tuhumarsa da shi.

Lauyan hukuma, Sifeto Awaisu Mohammed, ya bayyanawa kotu cewa Muhammad ya sace wadannan kayayyaki daga makwabtabsa Sanusi Bello da Abdulmalik Sani.

Lauyan ya kara da cewa makwabtan sun kai karansa ne ranan 20 ga watan Nuwamba, ofishin hukumar yan sandan dake Unguwan Rogo, jihar Sokoto.

Ya ce wannan halin bera ya sabawa dokar jihar kashi na 288.

KU KARANTA: An damke matar kwamandan Boko Haram, Mamman Nur ta kawo harin kunar bakin wake

A bangare guda, mun kawo muku rahoton cewa Al'ummomi da jama'ar gari da dama a jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya suna kaurace wa kasuwannin kauye saboda yadda wasu da ake kira 'yan sa-kai ko kuma kato-da-gora ke shiga suna kashe mutane da sunan farautar barayi da 'yan fashi.

Kasuwar Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara dake zaman daya daga cikin manyan kasuwannin na kauye da kuma ke ci a duk kowace ranar Lahadi na cikin wadanda ke fama da wannan matsalar kamar yadda wasu suka bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel