Gwamnatin tarayya ta haramta mana yin tafiya ne a shafukan jaridu - Ekweremadu, Bafarawa

Gwamnatin tarayya ta haramta mana yin tafiya ne a shafukan jaridu - Ekweremadu, Bafarawa

- Ike Ekweremadu da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa sun yi martani akan haramta masu fita kasashen waje da gwamnati tayi

- Sun bayyana cewa shafukan jaridu kawai suka ji cewar wai gwamnatin tarayya ta haramta masu fita kasashen waje

- Bafarawa ya bukaci gwamnati da ta je kotu idan har tana nufin shi da wani abu

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, a jiya sun bayyana cewa shafukan jaridu kawai suka ji cewar wai gwamnatin tarayya ta haramta masu fita kasashen waje.

Jiga-igan PDP din guda biyu sn bayyana cewa babu wani haramta masu fita waje da aka yi saboda basu samu kowani sako daga gwamnati kan hakan ba.

Kwamitin binciken shugaban kasa na musamman akan kudaden kasa da aka kwato ya bayyana a ranar Litin cewa ya gabatar da sunayen mutane 29 wadanda aka haramtawa tafiya kasashen waje biyo bayan shari’a da ake yi dasu akan rashawa.

Gwamnatin tarayya ta haramta mana yin tafiya ne a shafukan jaridu - Ekweremadu, Bafarawa

Gwamnatin tarayya ta haramta mana yin tafiya ne a shafukan jaridu - Ekweremadu, Bafarawa
Source: Depositphotos

Hakan ya biyo bayan wata sanarwa da aka yi a watan Oktoba lokacin da gwamnatin tarayya ta haramtawa wasu yan Najeriya 50 fita akan rashawa.

KU KARANTA KUMA: Hadimin Gwamna Obiano ya jagoranci kamfen din Buhari a kudu maso gabas

Ekweremadu a wani jawabi daga kakakinsa Uche Anichukwu a jiya yace labarin haramcin da aka sanya masa na yin tafiya karya ne.

A nashi bangaren, Bafarawa ya bayyana cewa idan har gwamnatin tarayya na da wani manufa a kanshi, toh taje kotu maimakon buga shi da sauran shugabannin adawa a shafukan jaridu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel