Tsohon shugaban PDP a Gombe tare da magoya bayansa 10,000 sun koma APC

Tsohon shugaban PDP a Gombe tare da magoya bayansa 10,000 sun koma APC

- Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Gombe, Adamu Yaro Gombe, ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC

- Yace shi da magoya bayansa sama 10,000 a fadin kananan hukumomi goma sha daya na jihar sun yanke shawarar barin PDP

- Yayi zargin cewa tsohuwar jam’iyyar nasa da masu ruwa da tsaki basa bashi girman da ya kamata a matsayinsa na tsohon shugaban jam’iyyar a jihar

Tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe, Adamu Yaro Gombe, ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yayinda yake jawabi ga manema labarai bayan ganawa da magoya bayansa, AY Gombe kamar yadda aka fi saninsa da shi yace shi da magoya bayansa sama 10,000 a fadin kananan hukumomi goma sha daya na jihar sun yanke shawarar barin PDP.

Tsohon shugaban PDP a Gombe tare da magoya bayansa 10,000 sun koma APC

Tsohon shugaban PDP a Gombe tare da magoya bayansa 10,000 sun koma APC
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa AY Gombem wanda ya taba zama mamba a kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP ya bayyana cewa sun yanke shawarar barin PDP e saboda abunda suka bayyana a matsayin hantara daga shugabannin jam’iyyar a matakin jihad a kasa baki daya.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya koka da ayyukan Kungiyar Amnesty International

A cewarsa shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki basa bashi girman da ya kamata a matsayinsa na tsohon shugaban jam’iyyar a jihar.

Tsohon jigon na PDP ya kara da cewa ya zabi komawa APC ne saboda kokarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu a shakaru uku da suka gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel