Hisbah ta damke mata 11 a bikin daurin auren yan madugo a jihar Kano

Hisbah ta damke mata 11 a bikin daurin auren yan madugo a jihar Kano

- A unguwar Sabon Gari, an daura aure tsakanin Safiya da Fatima

- Fitinan auren jinsi ya fara zama kalubale ga al'ummar Musulmi

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke tsala-tsalan mata 11 a unguwar Sabon Gari dake karamar hukumar Fagge a ranan Litinin, 17 ga watan Disamba kan shirya bikin daurin aure tsakanin mata biyu, jaridar Kano Today ta bada rahoto.

Babban hafsan hukumar Hisbah, Nasiru Ibrahim ya ce hukumar ta samu rahoton lekan asiri kan wata Safiya Yobe da zata auri wata Fatima Gezawa. Sai hukumar ta kai farmaki wajen shirya taron inda ta damke yan mata 11 tare amaryar da angon dukka mata.

Hisbah ta damke mata 11 a bikin daurin auren yan madugo a jihar Kano

Hisbah ta damke mata 11 a bikin daurin auren yan madugo a jihar Kano
Source: UGC

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya tafi kasar Nijar

Amma daya daga cikin wadanda aka kama mai suna, Fati Jariryar Zuciya, ta ce sun shirya wata liyafa ne domin nuna farin cikin nadin Fatima Gezawa a matsayin mataimakiyar shugaban kungiyar yan rawa, ita kuma mijinta Safiya Yobe ce shugabar kungiyar.

A shekarar 2007, wan samu irin wannan abu a jihar Kano inda wata mata mai suna 'Aunty Maiduguri' inda ta auri mata hudu kuma ta shirya taro domin tara kudi wa wata karuwa da zatayi aure.

Fitinar auren jinsi ya shigo Najeriya tun lokacin da kasashen ketare suka fara halalta auren jinsi a kasashensu. A yanzu akwai yar takarar shugaban kasa, Oby Ezekwesili, wacce tace zata baiwa kowa daman ya auri wanda ya ga dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel