Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon Manchester United ta sallami Jose Mourinho

Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon Manchester United ta sallami Jose Mourinho

Kungiyar kwallon kafan kasar ingila, Manchester United, ta sallami kocinta, Jose Mourinho, bayan kungiyar kwallon Liverpool ta lallasata a karshen makon da ya gabata a filin Anfield.

Shugabancin kungiyar kwallon kafan ta tabbatar da wannan labari ne a wata jawabi da suka saki. Jawabin yace:

"Manchester United na sanar da cewa kocinta Jose Mourinho, ya bar jam'iyyar daga yau. Wannan kungiya na nuna godiyarta ga Jose bisa ayyukan da yayi a zamansa a Manchester United kuma muna masa fatan alheri a rayuwa."

"Za'a nada sabon kocinta rikon kwarya zuwa karshe wannan kaka, yayinda za'a gudanar da aikin neman sabon koci na din-din-din."

Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon Manchester United ta sallami Jose Mourinho
Yanzu-yanzu: Kungiyar kwallon Manchester United ta sallami Jose Mourinho
Asali: Twitter

Jose Mourinho ya fara samun matsala ne da wasu mambobin kungiyar kwallon kafan musamman a wannan kaka. Da farko Paul Pogba wanda yake fito-na-fito da shi, sannan Antonio Valencia wannan aka tilasta ta bada hakuri don ya nuna yana son a sallami Mourinho."

Tsohon kocin FC Porto, Chelsea, Inter Milan da Real Madrid ya so tsayawa a Manchester har na tsawon shekaru 15 amma ko shekaru 3 bai karasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel