Wata sabuwa: Uwa daya ta haife mu ni da Shugaba Muhammadu Buhari - Atiku

Wata sabuwa: Uwa daya ta haife mu ni da Shugaba Muhammadu Buhari - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya daga shekara ta 1999 zuwa 2007 kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Shi dai shugaban na Najeriya a yau ne 17 ga watan Disemba ya cika shekaru 76 da haihuwa a duniya.

Legit.ng Hausa ta samu cewa Atiku Abubakar din a sakon da ya wallafa a shafinsa na Tiwita, ya ce yana taya shugaban kasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da ikirarin cewa uwa daya ta haife su watau Najeriya.

"Ina taya Shugaba @MBuhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa, kuma ni da iyalina muna masa addu'ar tsawon rai."

Ya kara da cewa: "Duk da cewa ni da shi za mu hadu a fagen zabe nan ba da jimawa ba, ina son tabbatar da cewa ni da shi 'yan uwan juna ne da kasarmu Najeriya ta haifa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel