Yadda kungiyoyin kwallo za su kara a zagayen gaba na cin kofin zakarun turai

Yadda kungiyoyin kwallo za su kara a zagayen gaba na cin kofin zakarun turai

Da ranar yau ne dai aka gudanar da zaben yadda jadawalin kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar turai zai su kara da junan su a ci gaba na gasar cin kofin zakarun turai da ake kan yi na kakar wasan shekarar 2018/2019.

Sai dai wasannin da suka fi daukar hankali da aka hada sune na kungiyar Liverpool da za ta hadu da zakarun Jamus Bayern Munich a zagaye na biyu a gasar zakarun Turai, yayin da kuma aka hada Manchester United da Paris St-Germain.

Yadda kungiyoyin kwallo za su kara a zagayen gaba na cin kofin zakarun turai
Yadda kungiyoyin kwallo za su kara a zagayen gaba na cin kofin zakarun turai
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Tsohon gwamna Fayose ya shiga sabuwar matsala

Za a yi karawa ta farko ne a ranakun 12 da 13 da 19 da 20 a watan Fabrairu, karawa ta biyu kuma a ranar 5 da 6 da 12 da 13 na watan Maris.

Ga dai yadda aka yi hadin nan:

Yadda aka hada kungiyoyin:

Schalke v Manchester City

Atletico Madrid v Juventus

Manchester United v Paris St-Germain

Tottenham v Borussia Dortmund

Lyon v Barcelona

Roma v Porto

Ajax v Real Madrid

Liverpool v Bayern Munich

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel