Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai shilla kasar Nijar gobe
- Bayan dawowa daga Poland, Buhari zai tafi Nijar
- Najeriya zata kwana gobe babu Buhari, babu Osinbajo a kasar
- Shima mataimakin shugaban kasa zai tafi kasar Jamus halartan wani taro
Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi birnin Zinder, kasar Nijar a gobe Talata, 18 ga watan Disamba, 2018.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki wannan jawabi ne a rana Litinin cewa Buhari zai yi tafiyar kwana daya domin halartan taron bikin murnan shekara 60 da samun jamhuriyyar Nijar.
Yace: "A gayyatan da shugaban kasan Nijar Mahamadou Issoufou, ya aikowa shugaba Buhari, zai zama bako na musamman a matsayinsa na makwabcin kasar Nijar."
"Wannan taron da shugaba Buhari zai halarta zai kara zurfafa alaka da zumunci tsakanin gwamnatocin biyu da yan kasashensu."
Wadanda zasu raka Buhari sune gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar; gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i; da gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola Isiaka na jihar Osun."
Sauran sune dogarinsa da karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Khadija Bukar Abba Ibrahim.”
Shugaba Buhari zai tafi ne bayan bikin murnar cikansa shekaru 76 a duniya da akayi a fadar shugaban kasa yau.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng