Yanzu-yanzu: An saki mutane 20 da ake zargi da kisa Janar Alkali a Jos

Yanzu-yanzu: An saki mutane 20 da ake zargi da kisa Janar Alkali a Jos

Labarin da ke shigo mana da dumi-dumi na nuna cewa alkalin kotun jihar Plateau, Jastis Daniel Longji ya baiwa mutane ashirin da ake zargi da kisan janar Ibrahim Alkali beli a yau Litinin, 17 ga watan Disamba, 2018.

An damke mutane 28 a watan Oktoba da zargin hannu cikin kisan Janar Idris Alkali wanda aka nema aka rasa a ranan 3 ga watan Satumba yayinda yake tafiya daga Abuja zuwa Bauchi.

Alkalin yace: "Na saurari jawaban lauyoyin kan bukatun beli. Karkashin doka mai lamba 100,138 da 148, zargi na 3, 4 da 5 da ake tuhumarsu dashi na boye gaskiya, kin son a nemi gawar marigayin ya sabawa doka. Amma da aka cajesu a lokacin, da yanzu sun gama zaman kurkuku."

"Amma sauran, bani da lokacin sauraron abubuwan da lauyoyin ke fada saboda takardun da aka kawo na da yawa. Sai na duba su."

Jastis Longji ya basu beli da tara miliyan 1 akan kowannensu, sannan sai an masu mai tsaya masu wanda ya kamata ya kasance mai anguwa kuma sai ya rantse.

An gurfanar da su kan laifuka biyar wanda ya shafi kisan kai, boye gaskiya, hana sojoji gudanar da binicke kan gawar marigayin.

KU KARANTA: Manufarmu na canza suna zuwa Legit.ng Hausa - Mudathir Ishaq, Editan Jaridar Legit Hausa

Mun kawo muku a bayan cewa binciken jami'an 'yan sandan jihar ta Filato shine ya tabbatar da alakar wadanda ake neman yanzu haka ruwa a jallo da batan sojan a watan Satumbar da ya gabata.

Legit.ng Hausa ta samu cewa cikin wadanda ake neman hadda basaraken garin na Dura Du, inda a nan ne aka gano motar ta Janar din a cikin wani kududdufi bayan tsotse ruwan dake ciki kwanakin baya.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Janar din ya bata ne lokacin da yake kan hanyar sa ta zuwa Bauchi amma kuma har yanzu ba'a gan shi ba. Sai dai hankulan jama'a da dama ya kadu bayan da aka gano motar sa tare da ta wasu a cikin kududdufi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel