Dakarun soji sun hallaka yan Boko Haram 4 a Maibukarti

Dakarun soji sun hallaka yan Boko Haram 4 a Maibukarti

Rundunar sojin hukumar Operation Lafiya Dole ta samu nasara kan wasu yan tada kayar bayan Boko Haram a ranan Lahadi, 16 ga watan Disamba, 2018 a kauyen Maibukarti, hanyar Maiduguri- Damboa a jihar Borno.

Jami'an soji sun hallaka akalla yan ta'addan guda hudu kuma sun kwato makamai da wasu kayan aikinsu.

Dakarun soji sun hallaka yan Boko Haram 4 a Maibukarti

Dakarun soji sun hallaka yan Boko Haram 4 a Maibukarti
Source: Facebook

Kakakin hukumar Sani Usman KK ya saki wannan jawabi ne inda yace:

"Rundunar Operation LAFIYA DOLE a ranan Lahadi, 16 ga watan Disamba 2018 sun hallaka yan Boko Haram hudu kuma sun kwato makamai. Yan ta'addan sun kai hari kauyen Maibukarti misalin karfe 5:00pm inda sukayi artabu da jami'an soji.

Jami'an sojin samu karin runduna kuma jami'an soji sama sun kawo dauki inda aka fitittiki yan ta'addan. Abin takaicin shine anyi rashin soja daya.

Jaruman sojin sun kwato bindigar AK47 4, harsasai carbin harsasan AK47 5, babura 2, keke 1."

Dakarun soji sun hallaka yan Boko Haram 4 a Maibukarti

Dakarun soji sun hallaka yan Boko Haram 4 a Maibukarti
Source: Facebook

KU KARANTA: Kada ka jira sai gobe: Dawo da shafin Legit.ng akan manhajar Opera cikin hanyoyi uku

Mun kawo muku rahoton cewa Mazauna garin Molai, wata kauye kusa da garin Maiduguri a jihar sun shiga cikin dar-dar yayinda ake artabu tsakanin rundunar sojin Najeriya da yan tada kayar bayan Boko Haram.

Wani mazauni ya bayyanawa manema labari ya cewa hukumar soji ta tura dakaru misalin mintuna 45 da suka wuce domin fitittikan yan ta'addan.

Molai kadai ce kauyen da ke yankin da ba'a kaiwa hari cikin watanni biyu da suka gabata ba. Kauyoyin Dalori, Konduga, Dala Shuwa, Dala Karamsu, Mammanti, Zabarmari, sun fuskanci hare-hare a kwanakin nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel