Zahra Buhari-Indimi ta rubuta sako mai sanyaya zuciya ga mahaifinta a ranar haihuwarsa

Zahra Buhari-Indimi ta rubuta sako mai sanyaya zuciya ga mahaifinta a ranar haihuwarsa

Yau Litinin, 17 ga watan Disamba yayi daidai da cikar shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari shekaru 76 a duniya sannan kuma masu fatan alkhairi da dama sun je shafinsu na zumunta domin yi masa fatan alkhairi ciki harda yarsa, Zahra Buhari-Indimi.

Kyakyawar yar tasa ta je shafinta na Instagram domin taya mahaifinta murna dauke da wani kayataccen hotonsa tare da uwargidansa, Aisha Buhari da kuma wani sako mai kayatarwa.

Zahra Buhari-Indimi ta rubuta sako mai sanyaya zuciya ga mahaifinta a ranar haihuwarsa

Zahra Buhari-Indimi ta rubuta sako mai sanyaya zuciya ga mahaifinta a ranar haihuwarsa
Source: Instagram

Ta rubuta: “Ina taya ka murnar zagayowar ranar haihuwarka ya mahaifina. Allah ya karo shekaru masu yawa cikin lafiya. Sannan kuma Allah ya albarkaci rayuwarka ta kowani hanya."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe 14 sun kuma raunata 17 a kauyen Kaduna

An haifi Buhari wanda ya ke shugabancin Najeriya a yanzu, a ranar 17 ga watan Disamba, 1942. Ya kasance tsoho manjo janar a rundunar sojin Najeriya sannan kuma yayi aiki a matsayin shugaban kasa daga ranar 1 ga watan Disamba 1983 zuwa ranar 27 ga watan Agustan 1985, bayan yakarbi mulki a juyin mulkin sojoji.

Barka da zagayowar ranar haihuwarka Shugaba Buhari!

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel