Mun yi nadamar zaben Buhari - Kungiyar matasan arewa

Mun yi nadamar zaben Buhari - Kungiyar matasan arewa

- Kungiyar matasan arewa ta nuna danasani akan zaben shugaban kasa Buhari da suka yi a 2015

- Shugaban kungiyar matasan arewa, Shettima Yerima, yace ya zama wajibi a gare su su nuna damuwa da bakin cikin su akan zaben makiyn yankinsu da suka yi

- Ya kara da cewa ya zama wajibi ayi taron Dangi a kawar da Buhari daga mulki a 2019

Rahotanni sun kawo cewa shugaban kungiyar matasan arewa, Alhaji Shettima Yerima, yace ya zama wajibi a gare su a matsayin su na shugabannin matasa a arewa, su nuna damuwa da bakin cikin su akan abinda ya kira zaben tumun dare da suka yi kuma suka sa mabiyansu su kayi ta hanyar zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda suka bayyana a matsayin mara kishin Arewa.

Mun yi nadamar zaben Buhari - Kungiyar matasan arewa
Mun yi nadamar zaben Buhari - Kungiyar matasan arewa
Asali: Depositphotos

Yerima ya kara da cewar, ko kadan Buhari bai dace da shugabancin Najeriya ba, domin a fili yake rikon kasar kamar Najeriya ta fi karfin Mutum irin Buhari, wanda bai da gogewa ta bangaren ilimi, ko harkokin kasuwanci, hakan ya sa kullum Arewa sai kara fuskantar koma baya take, Talauci na cigaba da kisan kare Dangi ga Jama'ar yankin, amma abin mamaki Buhari ko a Jikin shi, sai cigaba da harkokin gabansa yake, ya zama misalin makahon direba ya kwashi Jama'a zai kai ga halaka.

Shafin Rariya ta rahoto cewa Yerima ya kara da cewar ya zama wajibi ayi taron Dangi a kawar da Buhari daga mulki a 2019 kafin ya karasa kassara yankin Arewa, inda yace wannan shine babban dalilin da yasa sanannen Dattijon nan mai kishin Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya fito fili ya ankarar da Jama'a hatsarin cigaba da mulkin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Yau ne zagayowar ranar haihuwar Shugaban kasa Buhari

Ya kara da cewa babu abinda Buhari yayi na cigaba a Arewa, dukkanin ayyukan raya kasa an tattara su gaba daya a Jihohin Yarbawa, saboda Manyan Ma'aikatun Gwamnatin Tarayya uku a dauka an damkawa Mutum guda Bayarabe Fashola, wato Ma'aikatun Ayyuka da haske Wutar Lantarki da Gidaje, shin babu Dan Arewan da ya Cancanta ne wanda za'a dauki daya daga cikin Ma'aikatun nan a bashi ne? Amma maimakon a fahimci maganar Ango Abdullahi sai aka fito ana ta zagin shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel