Yau ne zagayowar ranar haihuwar Shugaban kasa Buhari

Yau ne zagayowar ranar haihuwar Shugaban kasa Buhari

- Yau 17 ga watan Disamba ne yayi daidai da zagayowar ranar haihuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya cika shekaru 76 a duniya

- Manyan ‘shuabannin Najeriya sun fara aika sakon taya murna ga shugaban kasar

- Jonathan ya ce Buhari ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa Najeriya hidima

A ranar yau 17 ga watan Disamba ne yayi daidai da zagayowar ranar haihuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya cika shekaru 76 a duniya.

Tuni a dai manyan ‘yan Najeriya suka fara taya shugaban kasar murnar, tare da addua’r Allah ya albarkaci rayuwarsa da kara masa lafiya.

Yau ne zagayowar ranar haihuwar Shugaban kasa Buhari

Yau ne zagayowar ranar haihuwar Shugaban kasa Buhari
Source: Depositphotos

Sai dai kuma da yawa sun yi amfani da damar wajen janyo hankalinsa ga halin matsi da kuncin rayuwa da ‘yan kasar ke ciki.

Yayin da manyan yan Najeriya kamar su, tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha suka fitar da sakonnin yi wa shugaban murnar zagayowar ranar haihuwar sa suka kuma yi masa addu’ar karin lafiya, talakawan Najeriya ma sun yi amfani da shafukan sada zumunta kamar su Facebook wajen yi masa fatan alkhairi.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari yayi murabus kan cewa da yayi wai tattalin arzikin kasa ya tabarbare – Atiku

Jonathan ya ce, Buhari ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa Najeriya hidima kasancewa ya yi aikin soja inda ya rike mukamin Gwamna, Minista, Shugaban kasa na mulkin soja da na farar hula da yake yi a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel