Ya kamata Buhari yayi murabus kan cewa da yayi wai tattalin arzikin kasa ya tabarbare – Atiku

Ya kamata Buhari yayi murabus kan cewa da yayi wai tattalin arzikin kasa ya tabarbare – Atiku

- Atiku Abubakar ya bayyana cewa abinda ya dace shugabaBuhari yayi shine yayi murabus kan kalaman da yayi game da tattalin arzikin Najeriya

- Buhari ya bayyana wa taron gwamnonin Najeriya cewa kowa ya kama kansa sa domin tattalin arzikin kasar nan na cikin wani irin mawuyacin hali

- Atiku ya ce gazawar Buhari da rashin kwarewar sa wajen jan ragamar mulkin kasa da saita tattalin arziki ya fito karara inda ya furta da bakin sa cewa a karkashin sa tattalin arzikin kasar nan ya durkushe

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa abinda ya dace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi shine yayi murabus kan kalaman da yayi game da tattalin arzikin Najeriya.

Idan za’a tuna Buhari ya bayyana wa taron gwamnonin Najeriya cewa kowa ya kama kansa sa domin tattalin arzikin kasar nan na cikin wani irin mawuyacin hali.

Buhari ya sanarwa da gwamnonin hakan ne a ganawar sirri da yayi da su a fadar shugaban kasa da yammacin ranar Juma’a, 14 ga watan Disamba.

Ya kamata Buhari yayi murabus kan cewa da yayi wai tattalin arzikin kasa ya tabarbare – Atiku
Ya kamata Buhari yayi murabus kan cewa da yayi wai tattalin arzikin kasa ya tabarbare – Atiku
Asali: Depositphotos

Shugaban kungiyar gwamnonin Najriya kuma Gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari wanda ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar HEDA ta nemi a binciki zargin da ke kan Gwamna Ganduje

Yace: “Buhari ya sanar da mu cewa kowa fa ya shiga hankalin sa saboda tattalin arzikin kasa ya fada cikin mawuyacin hali yanzu.”

Atiku ya kara da cewa gazawar Buhari da rashin kwarewar sa wajen jan ragamar mulkin kasa da saita tattalin arziki ya fito karara inda ya furta da bakin sa cewa a karkashin sa tattalin arzikin kasar nan ya durkushe.

“Duk shugaban da zai iya fadin haka kai tsayi kwanaki kadan kafin zabe na nuna cewa ya gaza ne ya na neman yayi amfani da wannan dama domin karkato da fuskokin ‘yan kasa don jingina gazawar sa ga haka.

“Amma kowa ya sani an ci bakin wuya a karkashin wannan mulki da Buhari sannan talauci sai kara yawa yake a tsakanin mutanen kasa. Buhari yaga babu mafita sannan gazawar sa ya fito fili karara ne ya sa kawai ta hakan ne zai bullo a tausaya masa."

Shua’aibu Phrank da ya fitar da wannan sako na Atiku ya ce yanzu ‘yan Najeriya sun waye kuma jiki magayi. Sun gane cewa Buhari da makarraban sa sun lafta wa ‘yan Najeriya karerayi ne kawai a 2015 amma yanzu kan mage ya waye.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel