Siyasa ba da gaba ba: Jonathan ya yabi Shugaba Buhari

Siyasa ba da gaba ba: Jonathan ya yabi Shugaba Buhari

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya shiga sahun masu taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar cika shekara 76 da haihuwa a cikin wani sako da ya fitar dauke da sa hannun sa.

Jonathan ya ce, Buhari ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa Najeriya hidima kasancewa ya yi aikin soja inda ya rike mukamin Gwamna, Minista, Shugaban kasa na mulkin soja da na farar hula da yake yi a yanzu.

KU KARANTA: Bidiyon sojoji suna kashe mutane ya bar baya da kura

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa tuni manya da jiga-jigai a harkokin mulki da siyasa a kasar suka soma kwararo sakkonnin taya murnar su ga shugaban kasar da ke cika shekaru 76 cif-cif a duniya ranar Litinin mai zuwa.

A wani labarin kuma, Wani faifan bidiyo da mu gama tantance sahihancin sa ba da kuma yake yaduwa a yanar gizo musamman ma dandalin sada zumunta tamkar wutar dauke da fuskokin wasu mutane sanye da kayan sojoji da kuma suka kashe wasu kauyawa na cigaba da jawo cece-kuce.

Faifan bidiyon dai kamar yadda muka samu, wani ma'abocin anfani da dandalin zumunta na Facebook ne mai suna Auwal Mustapha ya fara wallafa shi kafin daga bisani jama'a suyi ta yada shi suna kuma fadin albarkacin bakin su game da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel