Yanzu-yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Soji da Boko Haram a Borno

Yanzu-yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Soji da Boko Haram a Borno

Mazauna garin Molai, wata kauye kusa da garin Maiduguri a jihar sun shiga cikin dar-dar yayinda ake artabu tsakanin rundunar sojin Najeriya da yan tada kayar bayan Boko Haram.

Wani mazauni ya bayyanawa manema labari ya cewa hukumar soji ta tura dakaru misalin mintuna 45 da suka wuce domin fitittikan yan ta'addan.

Molai kadai ce kauyen da ke yankin da ba'a kaiwa hari cikin watanni biyu da suka gabata ba. Kauyoyin Dalori, Konduga, Dala Shuwa, Dala Karamsu, Mammanti, Zabarmari, sun fuskanci hare-hare a kwanakin nan.

Yanzu-yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Soji da Boko Haram a Borno
Yanzu-yanzu: Ana musayar wuta tsakanin Soji da Boko Haram a Borno
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa Soja guda daya ya mutu yayin da dakarun soji suka dakile wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram cikin kayan 'yan agaji suka kai masu a jihar Borno.

A sanarwar da mataimakin darektan hulda da jama'a na rundunar soji ta Ofireshon Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu, ya fitar ya bayyana cewar mayakan kungiyar Boko Haram din sun yi yunkurin shiga wani wani kauye bayan sun yi basaja cikin kayan 'yan agaji.

Nwachukwu ya Kara da cewar mayakan sun fake ne da rabon kayan agaji da ake yi a garin tare da bude wuta a kan tawagar soji dake wurin.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya cika shekaru 76 a duniya, kalli wankan da ya sha a yau (Bidiyo)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel