Da dumin sa: Jami'an DSS sun gurfanar da wani shugaban kungiyar 'yan a-ware na Biafra

Da dumin sa: Jami'an DSS sun gurfanar da wani shugaban kungiyar 'yan a-ware na Biafra

Jami'an hukumar rundunar 'yan sandan farin kaya na Department of State Services (DSS) sun samu nasarar cafkewa tare kuma da gurfanar da daya daga cikin jiga-jigan wata kungiya ta 'yan aware ta 'yan Biafra watau Biafra Zionists Federation (BZF), mai suna Benjamin Onwuka.

Kamar dai yadda muka samu, Barista Benjamin ya kai kusan wata biyar a hannun hukumar ta DSS tun bayan lokacin da suka cafke shi amma sai yanzu suka gurfanar da shi a gaban alkalin kotun tarayya dake a garin Owerri, jihar Imo.

Da dumin sa: Jami'an DSS sun gurfanar da wani shugaban kungiyar 'yan a-ware na Biafra
Da dumin sa: Jami'an DSS sun gurfanar da wani shugaban kungiyar 'yan a-ware na Biafra
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Ministan Buhari yayi magana game da cire tallafin mai

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa wani jigo a kungiyar ta 'yan aware Mista Mazi Ambrose Ugwo ya shaidawa manema labarai cewa a ranar a cikin satin nan ne dai aka gurfanar da shugaban na su.

Haka ma dai Mista Mazi ya yi kakkausar suka ga gwamnatin tarayya game da cigaba da tsare shugaban na su inda ya bayyana lamarin a matsayin abunda bai dace ba.

A wani labarin kuma, Wani magidanci mai shekaru 40 a duniya mai suna Reggies Chiyanke a yanzu haka kamar yadda muka samu labari yana kwance a wata asibiti yana karbar kulawar likita bayan da ya kwankwadi ruwan batir lokacin da ya kama matar sa da kwarto.

Majiyar mu dai ta shaida mana cewa wannan shine karo na biyu da shi magidancin yana shan ruwan batir bayan kama matar sa da kwarton wanda kusan a iya cewa halin matar ne bin maza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel