Burinmu shine Buhari ya samu kuri'u 2m a jihar Oyo - Shittu

Burinmu shine Buhari ya samu kuri'u 2m a jihar Oyo - Shittu

- Barrister Adebayo Shittu ya bayyana cewa zasu dauki matakan yakin zabe da zai baiwa Buhari nasa a 2019 ta hanyar tara masa kuri'u miliyan biyu a jihar Oyo

- Shittu ya ce ya ce a ranar 5 ga watan Janairu, 2019 za su fara yakin neman zabe daga tushe, don dinke duk wata baraka a tsakanin 'yayan jam'iyyar

- Dangane da makomar siyasarsa, Adebayo Shittu ya ce idan Allah na son al'ummar Oyo da alkairi, to kuwa komai daren dadewa sai ya zama gwamnan jihar

Barrister Adebayo Shittu wanda ya kasance ministan sadarwa, kuma daya daga cikin wadanda suka nuna sha'awar takarar kujerar gwamnan jihar Oyo karkashin jam'kiyyar APC ya bayyana cewa zasu dauki matakan yakin zabe da zai baiwa Buhari nasa a 2019 ta hanyar tara masa kuri'u miliyan biyu a jihar Oyo.

Shittu wanda jam'iyyar ta dakatar da tsayawa takararsa tun a zaben fitar da gwani, ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar na kasa Comrade Adams Oshiomhokle ne ya kulla makircin dakatar da shi don kawai cimma wata boyayyiyar manufa tasa.

Da jaridar Daily Trust ta tuntubi Shittu kan yadda yake kallon nasarar APC a jihar Oyo, la'akari da kirin rikicin da jam'iyyar ke fama da shi, ya ce a ranar 5 ga watan Janairu, 2019 za su fara yakin neman zabe daga tushe, don dinke duk wata baraka a tsakanin 'yayan jam'iyyar, tare da wayar da kan jama'ar jihar dangane da muhimmancin zabar Buhari/Osinbajo a karo na biyu.

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa muke son Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu

Burinmu shine Buhari ya samu kuri'u 2m a jihar Oyo - Shittu
Burinmu shine Buhari ya samu kuri'u 2m a jihar Oyo - Shittu
Asali: Twitter

Ya ce kima da darajar Buhari ta zarce ta jam'iyya a zukatan 'yan Nigeria, kasancewar "yana da masoya a cikin kowacce jam'iyyar skiyasar ta kasar, har da PDP, kuma kafataninsu zasu hadu ssu goya masa baya a zabe mai zuwa. Da karfin Allah zamu tara masa kuri'u miliyan biyu a jihar Oyo."

Dangane da makomar siyasarsa, Adebayo Shittu ya ce idan Allah na son al'ummar Oyo da alkairi, to kuwa komai daren dadewa sai ya zama gwamnan jihar. Ya ce yana da tabbacin cewa idan ya zama gwamna zai kawo gagarumin canji a jihar kasancewar ya shafe shekaru 40 yana siyasa.

"Kaf jihar Oyo babu wanda ke a irin kwarewata wajen fannin sadarwa. Zan yi amfani da tattara bayanai da kimiyar sadarwa wajen daga darajar jihar Oyo."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel