Farashin kayan abinci a Nigeria ya tashi da kashi 13.28 a watan Nuwamba - NBS

Farashin kayan abinci a Nigeria ya tashi da kashi 13.28 a watan Nuwamba - NBS

- Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta sanar da cewa an samu tashin farashin kayan abinci da na masarufi da kusan kashi 11.28 a ma'aunin CPI

- Hukumar ta lissafa wasu kayayyakin abinci da farashin nasu ya tashi a kasuwanni, wanda ya jawo hauhawar ma'aunin CPI har zuwa maki 11.28

- A baya, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa farashin kayan abinci ya sauka a kwaryar Kaduna

A yayin da farashin kayayyakin abinci da na masarufi ke ci gaba da tashin gwauron zabi a kasuwannin kasar, hukumar kididdiga ta kasa NBS ta sanar da cewa ma'aunin farashin kayan da jama'a suka fi saye CPI, ya yi nuni cewar an samu tashin farashin kaya da kashi 11.28 a ciki wata daya.

Hukumar na ganin cewa wannan tashin farashin kayan ya faru ne sakamakon kayan tashin farashin hatsi da na sarrafa nauyin biredi, madara, kwai da bota, kifi, kayan ganye, 'yayan itatuwa da kitse, dankalin turawa, doya da dai sauransu.

Akan kididdigar (wata bayan wata), sakin layin ma'aunin farashin abincin ya karu da kashi 0.90 a watan Nuwamba 2018, wanda ke nuni da karin maki 0.08 akan 0.82 da aka samu a watan Oktoba 2018.

KARANTA WANNAN: Daga karshe: Jam'iyyar SDP ta bayyana dalilin zabar Alhaji Shehu Gabam maimakon Dr Junaid

Farashin kayan abinci a Nigeria ya tashi da kashi 13.28 a watan Nuwamba - NBS

Farashin kayan abinci a Nigeria ya tashi da kashi 13.28 a watan Nuwamba - NBS
Source: Facebook

Mafi dai daito ko tsaka tsakiya na ma'aunin farashin kayan abincin na shekara, wanda aka kwashe watanni 12 da ya kare a Nuwambar 2018, tare da alakantashi da watanni 12 na bayam ya nuna cewa an samu kashi 14.80, kenan akwai karin farashin kayan da kusan kashi 11.28.

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi sun fadi warwas a kasuwannin da ke kwaryar Kaduna.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani rahoto da jaridar Daily Trust ta gudanar, a wasu manyan kasuwannni da ke kwaryar Kaduna. Sai dai, a yayin da farashin kayan wasu kayayyakin masarufin ya sauko, a hannu daya kuwa wasu sun tashi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel