Alkaliya Ajumogobia ta yanke jiki ta fadi a gaban Kotu

Alkaliya Ajumogobia ta yanke jiki ta fadi a gaban Kotu

Lamarin duniya dai da Hausawa kan ce ko wasso zaman lafiya shi ya so, mun samu rahoton wani abin mamaki da ya auku a babbar kotun jihar Legas, yayin da wata Mata abar zargi ta yanke jiki ana tsaka da fara gudanar da shari'a a kanta.

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, tsohuwar Mai Shari'a, Alkaliya Rita Ofili Ajumogobia, a ranar Juma'ar da ta gabata, ta yanke jiki ta fadi a gaban babbar kotun jihar Legas da ke zamanta a Ikeja.

Wannan lamari dai kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito, ya auku ne ana daf da shiga zaman kotun domin sauraron karar tsohuwar Mai Shari'ar bisa zargin ta da aikata laifuka na zamba da rashawa.

Alkaliya Rita Ofili Ajumogobia
Alkaliya Rita Ofili Ajumogobia
Asali: UGC

Ajumogobia ta gurfana gaban kotun bisa zargin ta da aikata barna a bakin aikin ta na shari'a, gami da rashawa da zambar dukiyar da ba bu gumin ta kamar yadda hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC ke tuhumarta.

Sai dai a yayin da kaddara ta rigayi fata, Alkaliya Rita ta yanke jiki ta fadi kasa wanwar a harabar kotun ta jihar Legas daf da fara sauraron kararta a jiya Juma'a.

KARANTA KUMA: Dole Buhari ya sha kasa a zaben 2019 - Jerry Gana

Ko shakka ba bu an yi gaggawar garzayawa da ita wani asibiti da manema labarai ba su damar sanin sunan sa ba. Hakan ya sanya Alkalin Kotun, Mai Shari'a Hakeem Oshodi, ya dakatar da sauraron karar biyo bayan rokon lauya mai kare ta, Mista Robert Clarke.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Dakarun sojin Najeriya da ke aiki ba bu dare ba bu rana, sun samar nasarar ragargazar wasu 'yan ta'adda da suka addabi mazauna yankunan karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel