Da duminsa: Osinbajo, Obi, da sauran 'yan takarar mataimakan shugaban kasa na tafka muhawara

Da duminsa: Osinbajo, Obi, da sauran 'yan takarar mataimakan shugaban kasa na tafka muhawara

A ci gaba da fuskantar zaben 2019 mai gabatowa, 'yan takara 5 ne ke ci gaba da tafka muhawarar da aka shiryawa abokan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyu 5, wanda ke kan gudana a otel din Transcorp Hilton da ke Abuja.

Kungiyar tafka muhawara kan zabe ta Nigeria NEDG tare da hadin guiwar kungiyar watsa labarai ta Nigeria BON, suka shirya wannan taron muhawarar.

Babban sakataren kungiyar tafka muhawara kan zabe ta Nigeria, Eddi Emesiri, ya zayyana jam'iyyun da suka hada da ACPN, ANN, APC, PDP da kuma YPP, daga cikin wadanda suke fafata wannan muhawarar.

KARANTA WANNAN: 2019: Wamakko ya bukaci 'yan Nigeria da su zabi Buhari tare da kaucewa shiga rikicin siyasa

Da duminsa: Osinbajo, Obi, da sauran 'yan takarar mataimakan shugaban kasa na tafka muhawara

Da duminsa: Osinbajo, Obi, da sauran 'yan takarar mataimakan shugaban kasa na tafka muhawara
Source: Twitter

Imoni Amarere, jami'in watsa labarai a tashar talabijin ta AIT, shi ke kula da wannan muhawara ta 'yan takarar mataimakan shugaban kasa da ake gudanarwa a yau.

Masu nazari da sharhi kan harkokin siyasa na hasashen cewa muhawarar zata fi mayar da hankali kan muhimman abubuwan da suka shafi kasar kama daga tattalin arzikin Nigeria, ilimi, kiwon lafiya, tsaron kasa da kuma harkokin kasashen waje.

Magoya bayan dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, na ci gaba da yin zanga zanga a wajen harabar da ake gudanar da taron, bisa rashin sanya abokin takararsa daga cikin masu tafka muhawarar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel