Ko anki ko anso: Tattalin arzikin Nigeria na cikin mawuyacin hali - Buhari

Ko anki ko anso: Tattalin arzikin Nigeria na cikin mawuyacin hali - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da gwamninin jihohi 36 na kasar nan, cewar tattalin arzikin kasar na cikin wani mawuyacin hali

- Haka zalika shugaban kasa Buhari ya bukaci gwamnonin da su zage damtse don farfado a tattalin arzikin tare da dorewarsa

- A hannu daya kuwa, gwamnonin suma sun godewa shugaban kasar na sakarwa jihohin kudaden Paris Club ba tare da tauye wani bangare daga ciki ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da gwamninin jihohi 36 na kasar nan, cewar tattalin arzikin kasar na cikin wani mawuyacin hali. Shugaban kasar dai ya gana da gwamnonin 36 ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma'a.

Da yake zantawa da manema labarai na cikin fadar shugaban kasar jim kadan bayan kammala ganawar, shuganan kungiyar gwamninin Nigeria NGF, Abdul'aziz Yari na jihar Zamfara ya ce shugaban kasar ya bukace su akan zage damtse.

Kan wannan bukata ta shugaban kasar, Yari ya ce: "Shugaban kasar dai ya fara ne da yin godiya a garemu, tare da sanar damu cewa lallai tattalin arzikin kasar na cikin wani mawuyacin hali kuma dole ne muyi aiki tare don samar da mafita akan hakan."

KARANTA WANNAN: Daga karshe: Jam'iyyar SDP ta bayyana dalilin zabar Alhaji Shehu Gabam maimakon Dr Junaid

Ko anki ko anso: Tattalin arzikin Nigeria na cikin mawuyacin hali - Buhari

Ko anki ko anso: Tattalin arzikin Nigeria na cikin mawuyacin hali - Buhari
Source: Twitter

Ya kuma yi nuni da cewa gwamnonin suma sun godewa shugaban kasar na sakarwa jihohin kudaden Paris Club ba tare da tauye wani bangare daga ciki ba.

Daga cikin wadanda suka halarci taron majalisar zartaswar, akwai David Umayi (Ebonyi),Abdullahi Umar Ganduje (Kano), Abdulfatah Ahmed (Kwara), Kashim Shettima (Borno), Atiku Bagudu (Kebbi), Emmanuel Udom (Akwa Ibom), Simon Lalong (Plateau), Abubakar Sani Bello (Niger), Gboyega Oyetola (Osun), Rotimi Akeredolu (Ondo), Nasiru El-Rufai (Kaduna) da Yahaya Bello (Kogi).

Haka zalika, akwai wasu mataimakan gwamnoni da suka samu damar halartar taron, da suka hada da mataimakin gwamnan jihar Katsina, Mannir Yakubu, da sauransu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel