Daga karshe: Jam'iyyar SDP ta bayyana dalilin zabar Alhaji Shehu Gabam maimakon Dr Junaid

Daga karshe: Jam'iyyar SDP ta bayyana dalilin zabar Alhaji Shehu Gabam maimakon Dr Junaid

- Jam'iyyar SDP ta bayyana dalilinta na sauya mataimakin dan takarar shugaban kasar jam'iyyar Dr Junaid da Alhaji Shehu Musa Gabam

- SDP ta ce wannan sauyin ya biyo bayan wani zama da shuwagabannin jam'iyyar na kasa suka gudanar, inda aka cimma yarjejeniya kan Dr Junaid ya janye

- Haka zalika jam'iyyar ta tabbatar da cewa, Dr Junaid zai ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan shuwagabannin jam'iyyar masu muhimmanci

A ranar Alhamis, shuwagabannin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), sun bayyana cewa an samu sauyin Dr Junaid a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar da Alhaji Shehu Musa Gaban ta hanyar cimma yarjejeniya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shuwagabannin jam'iyyar na kasa suka rabawa manema labarai a daren ranar Juma'a a Abuja, ta hannun sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa, Alhaji Alfa Mohammed.

Sanarwar ta ce: "an karkato hankulanmu kan wani labari da ake yadawa a kafafen sadarwa na zamani kan batun sauya Dr Junaid a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarmu mai albarka ta SDP.

KARANTA WANNAN: Bukukuwan kirsimeti: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a Kaduna

Dr Junaid Muhammad

Dr Junaid Muhammad
Source: Depositphotos

"An canja Dr Junaid bayan wani taron tattaunawa da shuwagabannin jam'iyyar na kasa suka gudanar wanda kuma shima yana a ciki, kuma a taron aka cimma matsayar cewa zai janye don cimma wasu kudurorin siyasa na jam'iyyar.

"Don haka a matsayin sa na dan jam'iyya nagari, ya janye takararsa, kamar yadda ya sanar; kuma ya sanya hannu kan dukkanin wasu takardu da hukumar INEC ta bukata don bin doka da oda.

"Zai ci gaba da kasancewa mutum mai matukar muhimmanci da daraja a cikin shuwagabannin jam'iyyar. A hannu daya kuwa, an maye gurbinsa da Alhaji Shehu Musa Gabam, daga shiyyar Arewa maso Gabas."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel