An gudanar da jana'izar sojoji 23 da aka kashe a Metele (Hotuna)

An gudanar da jana'izar jami'an hukumar sojin Najeriya 23, yawancinsu sun hallaka ne a mumunan harin da yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suka kaiwa soji a garin Matele inda aka hallaka da dama a cikinsu.

An birnesu ne yau Juma'a, 14 ga watan Disamba a babban birnin jihar Borno, Maiduguri.

Hotunan da Legit.ng Hausa ta samu ya nuna yadda aka gudanar da jana'izar tare da iyalan jaruman sojin da hukumar ta rasa.

Mun kawo muku rahoton cewa daya daga cikin sojojin da suka tsira daga harin da Boko Haram suka kai wa barikin Metele dake karamar hukumar Guzamala a jihar Barno ya bayyana wa majiyarmu ta Premium Times yadda 'yan ta'addan suka yi nasarar yi masu ta'asa a farkon satin nan a barikin su dake a garin Metele.

Sojan wanda ya bukaci a sakaya sunan sa yace shi ma Allah ne ya sa zai tsira da ran sa a wannan hari domin kuwa sojojin Nijeriya da ke aiki a wannan bariki basu ji da dadi ba.

Kalli hotunan:

An gudanar da jana'izar sojoji 23 da aka kashe a Metele (Hotuna)
An gudanar da jana'izar sojoji 23 da aka kashe a Metele (Hotuna)
Asali: Facebook

An gudanar da jana'izar sojoji 23 da aka kashe a Metele (Hotuna)
An gudanar da jana'izar sojoji 23 da aka kashe a Metele (Hotuna)
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel