Maniyyata 95,000 za suyi aikin hajjin bana - Hukumar jin dadin alhazai

Maniyyata 95,000 za suyi aikin hajjin bana - Hukumar jin dadin alhazai

- Abun ba wuya, har an fara shirye-shiryen hajjin 2019

- Kamar bara, an baiwa Najeriya daman gabatar da maniyyata 95,000

- Kana ba'a dage haramcin shigo da goro kasar ba

A ranan Laraba, 12 ga watan Disamba, 2018 ma'aikatar aikin hajji da Umrah na kasar Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeru 95,000 a aikin hajjin 2019. wannan ya bayyana ne bayan yarjejeniyar fahimta da Najeriya tayi da kasar Saudiyya.

Game da jawabin da mai magana da yawun hukumar jin dadin alhazan Najeriya wato NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta saki, an yi yarjejeniyar ne a ma'aikatar hajji da Umrah a Saudiyaa karkashin jagorancin Ministan Hajji da Umarah, Dakta Muhammad Saleh bin Taher Benten da karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Khadija Bukar Abba Ibrahim.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya na ganawa da Shugaban Kasa Buhari

A wannan yarjejeniya, kasar Suadiya ta baiwa Najeriya damar gabatar da mahajjta 95,000 kamar na hajjin bara.

Dakta Taher Benten ya jinjinawa hukumar jin dadin alhazai kan yadda suka gudanar da aikin hajjin bara.

A bangare guda, a wata zama da shugaban hukumar NAHCON, Abdullahi Mukhtar Muhammad, yayi da mataimakin ministan Hajji da Umarah na Saudiyya, Hussain Ibn Naser Alsharrif, hukumar ta bukaci Saudiyya ta dage kudi Riyal 2,000 kan mahajjata da suka halarci hajji fiye da daya cikin shekaru biyar

Ma'aikatan kasar Saudiyyan sun jaddada haramcin shigo da goro cikin kasar da mahajjatan Najeriya keyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel