Bukukuwan kirsimeti: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a Kaduna

Bukukuwan kirsimeti: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a Kaduna

- Kayayyakin abinci na ci gaba da faduwa kasa warwas a kwaryar jihar Kaduna, a yayin da bukukuwan kirsimeti ke ci gaba da gabatowa

- Ana sayar da awon gero akan N200 maimakon N250 da ake sayar da shi a baya, sai kuma awon garri akan N150, maimakon N200 da ake sayar da shi a watan da ya gabata

- Sai dai, farashin lita 25 na man-ja ya tashi daga N6,500 zuwa N12,600. Sai kuma buhun albasa mai nauyin 50kg ya tashi daga N30,000 zuwa N35,000

A yayin da bukukuwan kirsimeti ke ci gaba da gabatowa, farashin wasu kayayyakin abinci da sauran kayan masarufi, sun fadi kasa warwas, yayin da farashin wasu kayan ya dai-daita tun a watan baya, a cikin kwaryar jihar Kaduna.

Wani rahoton bincike da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya hada a babbar kasuwar Kaduna a ranar Laraba, ya bayyana cewa farashin shinkafa, wake, gero, masara, alkama, tumatur, barkono da sauransu, ya sauko kasa sosai.

Ana sayar da buhun shinkafa yar gida mai nauyin 100kg akan N27,000 ko N28,000 yayin da ake sayar da buhu mai nauyin N100kg na farin wake akan N25,000 maimaikon N30,000 da ake sayar da shi watan da ya gabata.

KARANTA WANNAN: Okorocha ya gabatar da N276bn a matsayin kasafin kudin 2019

Bukukuwan kirsimeti: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a Kaduna
Bukukuwan kirsimeti: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a Kaduna
Asali: Facebook

Ana sayar da awon gero akan N200 maimakon N250 da ake sayar da shi a baya, sai kuma awon garri akan N150, maimakon N200 da ake sayar da shi a watan da ya gabata.

Haka zalika, ana sayar da kwandon tumatur da tarugy akan N5,000 da N5,500 akan N6,500 da N7,000 da ake sayar da shi a watan da ya gabata.

A daya hannun kuwa, farashin buhun gari na Semovita mai nauyin 25kg ya dai daita daga N2,900 zuwa N3,000, sai kuma ledar maggi mai 50 a ciki, ana sayar da shi akan N400 maimakon N380.

Sai dai, farashin lita 25 na man-ja ya tashi daga N6,500 zuwa N12,600. Sai kuma buhun albasa mai nauyin 50kg ya tashi daga N30,000 zuwa N35,000.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawaira ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel