Me yankan kauna: Mata ta fada cikin kabarin mijinta don hana binne shi, hotuna

Me yankan kauna: Mata ta fada cikin kabarin mijinta don hana binne shi, hotuna

Sha'anin binne wani mutum a wata makabarta dake garin Bahari a yankin Nakuru ya gamu da tsaiko na fiye da sa'o'i biyu biyo bayan muhawara a kan ko a binne shi ko a fasa.

Hayaniya ta barke a wurin binne marigayin bayan matar sa da wasu 'yan uwansa biyu sun daka tsalle sun fada cikin kabarin da aka haka yayin da malamin addini ke gudana da addu'o'i kafin a saka akwatun gawar mamacin cikin kabarin.

Matar mamacin da 'yan uwansa biyu sun ce sai dai a binne su tare da mamacin matukar ba za a mayar da gawar sa dakin ajiyar gawa ba.

Me yankan kauna: Mata ta fada cikin kabarin mijinta don hana binne shi, hotuna
Me yankan kauna: Mata ta fada cikin kabarin mijinta don hana binne shi, hotuna
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kwanan nan ta'addanci a Zamfara zai zama tarihi - Buratai ya ci al washi

Marigayin, Edward Mwangi, an kashe shi ne ranar 3 ga watan Disamba kuma an tsinci gawar sa washegari kusa da gidan mutumin da ake zargin ya kashe shi

Majiyar mu ta shaida mana cewar marigayi Mwangi tare da wasu abokansa biyu sun dira gidan mutumin da ya kashe shi bayan gano cewar masoyiyarsa da suka shafe fiye da shekaru 10 na cikin gidan.

Me yankan kauna: Mata ta fada cikin kabarin mijinta don hana binne shi, hotuna
Me yankan kauna: Mata ta fada cikin kabarin mijinta don hana binne shi, hotuna
Asali: Facebook

Sai dai reshe ya juye da mujiya bayan mutumin ya yi nasarar kwatar wuka daga hannun su Mwangi, wukar da ya yi amfani da ita wajen kisan Mwangi.

Me yankan kauna: Mata ta fada cikin kabarin mijinta don hana binne shi, hotuna
Me yankan kauna: Mata ta fada cikin kabarin mijinta don hana binne shi, hotuna
Asali: Facebook

Sakamakon bincike ya tabbatar da cewar Mwangi ya mutu ne sakamakon ciwukan yankan wuka da ya samu a jikinsa.

Da take bayyana bacin ranta, Mary, matar Mwangi ta ce gara a binne ta tare da mijinta tunda 'yan sanda sun sallami mutumin da ya kashe shi bayan sun tsare shi na wucin gadi.

Sai dai duk da goyon bayan mutanen kauyensu da Mary ta samu, hakan bai hana a binne gawar marigayi Mwangi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng