Mun dawo daga rakiyar duk wani furuci na Obasanjo - Fadar Shugaban Kasa

Mun dawo daga rakiyar duk wani furuci na Obasanjo - Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa, tuni ta dawo daga rakiyar duk wani kalami da zantuttukan bayyana ra'ayi na tsohon shugaban kasa Cif Olusugen Obasanjo, inda ta ce ba su da muhimmanci ballantana cancantar kulawa.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, fadar shugaban kasa Buhari ta bayyana cewa, a halin yanzu duk wani lafazi na tsohon shugaban kasa tamkar shagulantan bangaro ne da ba ya da wata cancanta da waiwaye ko sanya idanun lura a gare su.

Yayin ganawarsa da manema labarai a yau Laraba cikin babban birnin kasar nan na tarayya, kakakin fadar Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa, duk wanda tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ke da muradin goyon baya a zaben 2019 ya rage gare shi, domin kuwa ba yau farau ba sauye-sauyen wannan ra'ayi ba sabon furuci ba ne a kunnuwan al'ummar kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kakakin fadar ya ci gaba da cewa, tsohon shugaban kasa Obasanjo a yau yana iya bayyana goyon bayan sa ga dan takara guda kuma cikin kankanin lokaci ya sauya ra'ayi a yayin da ya so hakan.

Mun dawo daga rakiyar duk wani furuci na Obasanjo - Fadar Shugaban Kasa
Mun dawo daga rakiyar duk wani furuci na Obasanjo - Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

Mallam Garba ya kara da cewa, ba bu wani mamaki dangane a yadda tsohon shugaban kasa ya bayyana ra'ayinsa na rashin zabi cikin 'yan takarar zaben 2019 a wani taro da ya halarta a karshen makon da ya gabata, inda bayan kwana guda kuma ra'ayin sa ya sha bamban.

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasar yayin halartar wani taron kasa na 'kabilarsa ta Yarbawa cikin jihar Osun ya bayyana matsayarsa ta cewa ba ya wani zabi cikin 'yan takarar kujerar shugaban kasa na zaben badi.

KARANTA KUMA: Sai mun kunyata Gwamnoni da suka gaza sauke nauyin bashin albashin ma'aikata - Kungiyar Kwadago

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a sanadiyar wannan lamari ya sanya fadar shugaban kasa ta ce tuni ta daina bayar da wani muhimmanci ga lafuzan tsohon shugaban kasa Obasanjo da ba su da wani tasiri a bisa ma'auni na cancatar kulawa ko muhimmanci.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, a yau dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta gudanar da babban zaben kasa na 2019 cikin lumana da kwanciyar hankali.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng