Bincike: Jami'an tsaro ke mayar hannun agogon yaki da Boko Haram baya, suna kai musu abinci da man fetur

Bincike: Jami'an tsaro ke mayar hannun agogon yaki da Boko Haram baya, suna kai musu abinci da man fetur

Wani binciken jaridar The Next Edition ta bada rahoton cewa jami'an tsaron Najeriya ne ke mayar da hannun yaki da Boko Haram baya yayinda suke taimkawa wajen kaiwa yan Boko Haram tankokin man fetur.

Jaridar a dogon binciken da suka gudanar sun bayyana cewa sojoji, yan sanda, jami'an kwastom, jami'an shiga da fice da na NSCDC suna karban cin hanci hannun yan kasuwan da yan fasa kwabrin man fetur da kayayyakin masarufi masu kaiwa yan Boko Haram a kasashen ketare.

A tattaunawar da akayi da wasu jami'an tsaro, yan kasuwa da yan leken asirin, jaridar ta samu cikakken bayani kan yadda ake gudanar wannan kasuwancin da ke kawo cikas cikin yaki da Boko Haram da aka kai shekaru tara anayi yanzu.

tankan mai
Tankan man da aka fitar
Asali: Facebook

Majiyoyi masu karfi da aka sakaye sunayensu sun bayyana cewa akalla tankokin man fetur 60 da na kayayyakin masarufi 60 ake fitarwa daga kasar ta hanyar jihar Adamawa kulli yaumin.

KU KARANTA: Mahaifi dan shekara 58 ya yiwa diyarsa fyade

Jaridar ta samu labarin cewa yan Boko Haram na samun kayan abincinsu cikin wadannan kayayyakin da ake fitarwa ta barauniyar hanya.

A kowace rana, jami'an sojoji, yan sandan, jami'na shiga da fice, jami'an kwastam da na farin hula da aka tura iyakoki a jihar Adamawa na karban cin hanci daga N500 zuwa N30,000 daga hannun direbobi.

Sai su fitar da tankokin man su sayarwa yan Boko Haram ko su fitar da shi kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Bincike: Jami'an tsaro ke mayar hannun agogon yaki da Boko Haram baya, suna kai musu abinci da man fetur
Kayan abincin da ake fitarwa
Asali: Facebook

A yau, ana sayar wadannan man feturin a kasashen irinsu Kamaru, Nijar, Chadi da CAR. Wadannan kayayyaki ne yan Boko Haram suka dogara da shi da kuma kawo hare-hare cikin gari.

Bincike: Jami'an tsaro ke mayar hannun agogon yaki da Boko Haram baya, suna kai musu abinci da man fetur
Bincike: Jami'an tsaro ke mayar hannun agogon yaki da Boko Haram baya, suna kai musu abinci da man fetur
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng