Da dumi dumi: Yan ta'adda sun kai sabon hari a kauyen Zamfara, mutane 22 sun mutu

Da dumi dumi: Yan ta'adda sun kai sabon hari a kauyen Zamfara, mutane 22 sun mutu

- Wasu 'yan ta'adda sun kai hari a kauyen Malikawa da ke gundumar Gidan Goga,a jihar Zamfara, wanda kuma shine karo na biyu da suka kai harin a cikin 'yan watanni

- Wannan sabon harin da 'yan ta'addan suka kai ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 22, yayin da da dama daga jama'ar kauyen suka samu raunuka

- Wani mazaunin kauyen ya tabbatar da faruwar lamarin tare da yin sharhi kan yadda komai ya faru

Rahotannin da muka samu, na nuni da cewa wani sabon hari da wasu 'yan ta'adda suka kai a kauyen Malikawa da ke gundumar Gidan Goga, karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 22 yayin da wasu da dama suka jikkata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mazauna kauyen ne suka tabbatar da afkuwar wannan hari a ranar Talata, 11 ga watan Disamba, inda wasu 'yan bindiga da suka haura dozin suka budewa jama'a wuta bayan shigarsu kauyen a kan mashina.

"Ina kan hanyata ta komawa gida daga gona da misalin karfe 4 na yamma, sai na yanke shawarar in yi wanka; a cikin makewayin ne, na fara jiyo hayaniyar jama'a suna neman dauki. Na fito da hanzari inda na ke jiyo kararar harbe harben bindigogi, ga jama'a ta ko ina ana gudun ceton rai.

KARANTA WANNAN: Ya jawa kansa: Wani dan majalisa ya rasa kujerarsa bayan sauya sheka daga APC zuwa PDP

Da dumi dumi: Yan ta'adda sun kai sabon hari a kauyen Zamfara, mutane 22 sun mutu
Da dumi dumi: Yan ta'adda sun kai sabon hari a kauyen Zamfara, mutane 22 sun mutu
Asali: UGC

"Kafin nayi wani yunkuri na neman hanyar tsirada rayuwata, tuni 'yan ta'addan suka iso kofar gida na. Yadda na kubuta a wannan hali, ba zan iya tunawa ba," a cewar wani mazaunin kauyen wanda aka ruwaito yana bayyana yadda harin ya faru, inda yace akwai mutane 6 da suka boye a cikin kwabson gero, wadanda 'yan ta'addan suka cinnawa wuta, suka kone kurmus.

"A yanzu da nake maku magana, ina kauyen Boko, ina neman 'yayana da suka bace. Bamu gansu ba tun a jiya, sai dai mun binne gawarwakin wadanda suka mutu," a cewarsa.

Rahoton ya bayyana cewa duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin rundunae 'yan sanda na jihar, SP Muhammad Shehu, ya ci tura, har zuwa wannan lokaci da aka wallafa labarin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng