Mama Taraba ta koma jam'iyyar PDP

Mama Taraba ta koma jam'iyyar PDP

Tsohuwar ministar harkokin mata a gwamnatacin shugaba Buhari, Sanata Aisha Jummai Alhassan, wacce akafi sani da Mama Taraba ta sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples democratic Party PDP a ranan Talata, 11 ga watan Disamba, 2018.

Ta sake fita daga jam'iyyar UDP da ta koma ba da dadewa ba.

Mun kawo muku cewa Tsohuwar minister harkokin mata, Sanata Aisha Jumma Alhassan, ta sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC, zuwa jam’iyyar United Democratic Party, UDP.

Sanata Jummai wacce akafi sani da Mama Taraba ta yi murabus daga kujeran minister shugaba Buhari a yau sakamakon hanata takara kujeran gwamnan jihar Taraba da jam’iyyar APC tayi.

Hotuna: Mama Taraba ta koma jam'iyyar PDP
Hotuna: Mama Taraba ta koma jam'iyyar PDP
Asali: Facebook

A sakatariya jam’iyyar UDP, Mrs Alhassan ta bayyana cewa ta fita daga jam’iyyar APC ne saboda rashin adalci da akayi mata.

Bayan sauya shekanta daga APC, Aisha Alhassan (Mama Taraba) ta kwace kwamfutoci da kujeru da ta bawa ofishin APC da ke Jalingo a matsayin gudunmawarta.

Sakataren yadda labarai na APC a jihar, Mr Aaron Artimas ya ce Mama Taraba ta kuma kwace na'urar sanyaya daki wato AC da tebura da carpet da ta siyawa jam'iyyar kafin ficewar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel