Da duminsa: Jam'iyyu 5 da zasu kara a muhawara takaran shugaban kasa ranar Juma'a

Da duminsa: Jam'iyyu 5 da zasu kara a muhawara takaran shugaban kasa ranar Juma'a

Kungiyar shirya muhawarar zaben Najeriya NEDG da kungiyar kafofin yada labaran Najeriya BON ta saki sunayen jam'iyyu biyar da zasuyi muhawarar takarar kujeran mataimakin shugaban kasa da na shugaban kasa.

Game da jawabin da sakataren kungiyar, Mr Eddi Emesiri, ya saki, ya ce jam'iyyar Allied Congress Party of Nigeria (ACPN), Alliance for New Nigeria (ANN), All Progressives Congress (APC), Peoples Democratic Party (PDP) da Young Progressives Party (YPP) ne aka zaba.

Za'a gudanar da muhawarar masu takaran kujeran mataimakin shugaban kasa rana Juma'a, 14 ga watan Disamba, 2018 misalin karfe bakwia na yamma a `Transcorp Hilton, kuma za'a gudanar da na shugaban kasa ranan Asabar, 19 ga watan Junairu, 2019.

KU KARANTA: Gobara a babban cocin Katolika

Za'a nuna wannan muhawara a dukkan tashohin Najeriya da kuma a kafofin ra'ayi da sada zumunta.

Wadanda za'ayi muhawarar da su sune:

Farfesa Yemi Osinbajo na jam'iyyar APC

Mr Peter Obi na jam'iyyar PDP

Umma Getso na jam'iyyar YPP

Alhaji Abdulganiyu Galadima na ACPN

Abdullahi Iya na jam'iyyar ANN

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng