Dalilin da yasa naki halartan taron yarjejeniyar zaman lafiya - Atiku
- Shugaba Buhari ya halarci taron yarjejeniya tsakanin yan takaran shugaban kasa
- An nemi babban abokin hamayyar Buhari an rasa a taron
- Mamban kungiyar, Mathew Kuka ya karyata maganar cewa absu gayyaci Atiku ba
Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, ya bayyana a yau cewa bai samu goron gayyatar zaman rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yan takaran kujeran shugaban kasa a zaben 2019.
Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe, ya bayyana cewa "Ina tabbatar muku da cewa Atiku bai samu takardan gayyata.
Mun kawo muku rahoton cewa An nemi dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, an rasa a bikin rattaba hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya na dukkan yan takaran shugaban kasa a 2019 a farfajiyar ICC da ke birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Buhari ya rattaba hannu kan yarjejeniyar yan takaran shugaban kasa
Da farko ba'a san ainihin dalilin da ya hana Atiku Abubakar, wanda ya kasance babban abokin hamayyar shugaba Muhammadu Buhari zuwa ba.
Kana wasu yan takara irin Oby Ezekwesili da Omoyele Sowore basu halarci taron ba. Su ma dai sun bayyana cewa basu samu takardan gayyata ba.
Mamban kungiyar zaman lafiyan, Bishop Matthew Kukah, ya bayyanawa manema labarai cewa lallai sun mika sakon gayyata ga Atiku Abubakar wanda shine babban abokin hamayya a wannan zabe.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng