Babbar magana: Sojoji 11 na fuskantar tuhuma a kotun ladabtar da jami'an soji
- Sojoji 11 ne ke fuskantar tuhuma a wata kotu ta musamman da aka kafa don ladabtar da jami'an soji, wacce ke Enugu
- Kotun ladabtar da jami'an sojin mai dauke da mambobin 8, an kafa ta ne don tabbatar da wanzuwar ladabtarwa a tsakanin jami'an sojin da suka aikata laifi
- Sojojin da ake tuhumar su 11, an kamasu da aikata laifuka daban daban da suka hada da rashin kammala aikin sa aka sa mutum, bijirewa bin umurni da sauransu
Sojoji 11 ne ke fuskantar tuhuma a wata kotu ta musamman don ladabtar da jami'an soji, wacce babban kwamanda GOC na rundunar sojin kasa ta 82, da ke Enugu, Manjo-Janar Emmanuel Kabuk ya kafa a ranar Litinin.
Kabuk wanda ya kafa kotun ladabtar da jami'an sojin mai dauke da mambobin 8, ya ce ya kafa kotun ne don tabbatar da wanzuwar ladabtarwa a tsakanin jami'an sojin da suka aikata laifi.
Ya ce a yanzu haka kotun ladabtar da jami'an sojin ta fara tuhumar wasu sojiji 11 da aka kamasu da aikata laifuka daban daban da suka hada da rashin kammala aikin sa aka sa mutum, bijirewa bin umurni da sauransu.
KARANTA WANNAN: Gaskiya karara: Sake zabar Buhari a 2019 zai zama babbar musiba ga 'yan Nigeria - Obasanjo

Asali: Depositphotos
"Wannan kotun ta musamman an kafa ta ne don tabbatar da wanzuwar ladabci a tsakanin jami'an soji da ofisoshinsu na wannan runduna. Hakika ana bukatar ladabi a cikin wannan aiki ma damar a na son cimma bukatun da aka sa gaba, kamar yadda hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai ya bukata, da zummar yin garambawul ya aikin sojin kasar," a cewarsa.
Ya tabbatarwa sojojin da ake tuhumarsu, cewar kotun zata yi masu adalci ta hanyar basu damar kare kawunansu.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng