Gaskiya karara: Sake zabar Buhari a 2019 zai zama babbar musiba ga 'yan Nigeria - Obasanjo

Gaskiya karara: Sake zabar Buhari a 2019 zai zama babbar musiba ga 'yan Nigeria - Obasanjo

- Olusegun Obasanjo ya ce sake zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu zai kara iza wutar yunwa tare da kuncin da 'yan Nigeria ke fuskanta a halin yanzu

- Ya kuma karyata rahotannin da ake yadawa na cewar zai kasance dan kallo a zaben 2019 ba tare da daukar bangaranci tsakanin PDP ko APC ba

- Wata sanarwa daga mai magana da yawun Obasanjo ta ce Chief Obasanjo ba wawa bane da zai nade hannu yana ci gaba da kallon maha'intan kasar suna cin karensu ba babbaka

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce sake zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu zai kara iza wutar yunwa da talauci tare da kuncin da 'yan Nigeria ke fuskanta a halin yanzu.

Ya kuma karyata rahotannin da ake yadawa na cewar zai kasance dan kallo a zaben 2019 ba tare da daukar bangaranci tsakanin PDP ko APC ba, yana mai cewa "Wawa ne kadai zai tsaya a iyaka ba tare da shiga wani bangare ba."

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan a matsayin martani ga wani rahoto da aka fitar na cewar ya janye goyon bayan da ya fara yiwa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP.

KARANTA WANNAN: Majalisar dattijai ta biya Sanata Dariye alawus na N85.5m duk da yana garkame a kurkuku

Gaskiya karara: Sake zabar Buhari a 2019 zai zama babbar musiba ga 'yan Nigeria - Obasanjo
Gaskiya karara: Sake zabar Buhari a 2019 zai zama babbar musiba ga 'yan Nigeria - Obasanjo
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa, daga hannun Kahinde Akinyemi, mai magana da yawun Obasanjo, ya ce tsohon shugaban kasar ya dai bukaci 'yan Nigeria ne kawai su zabi 'yan takarar da suka dace a 2019, musammab a kujerar shugaban kasa.A cikin wata sanarwa, daga hannun Kahinde Akinyemi, mai magana da yawun Obasanjo, ya ce tsohon shugaban kasar ya dai bukaci 'yan Nigeria ne kawai su zabi 'yan takarar da suka dace a 2019, musammab a kujerar shugaban kasa.

Sanarwar ta ce: "A lokacin da Chief Olusegun Obasabjo ya ke kasar Cairo wajen halartar bukin baje koli na kasashen Afrika, wanda shine shugaban mashawartar hukumar shirya bukin, ya samu labarin cewa ana kamfanin dillancin labarai na kasa NAN na yada jita jitar wai ya koma dan kallo a siyasar kasar."

"Wawa ne kadai zai tsaya a tsakiyar iyaka bayan yana kallo ana lalata kasarsa, cin hanci na kara karuwa, babu makoma, babu tsaro, ana raba mukamai tsakanin 'yan uwa da abokai, tauye hakki da dai sauransu. Chief Obasanjo ba wawa bane da zai nade hannu yana ci gaba da kallon maha'intan kasar suna cin karensu ba babbaka," a cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel