Ruwan wuta: Gwamnati ta sayi jiragen yaki 30, masu saukar angulu 6 domin yakan Boko Haram

Ruwan wuta: Gwamnati ta sayi jiragen yaki 30, masu saukar angulu 6 domin yakan Boko Haram

Babban hafsan hukumar sojin saman Najeriya, Air Mashal Sadique Abubakar, a ranan Asabar a jihar Kano ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta sayi sabbin jirage 18, kan guda 12 da masu saukar angulu 6 da akayi oda.

Air Mashal Sadique wanda ya koma yankin Arewa maso gabas bisa ga umurnin shugaba Buhari domin kawar da yan Boko Haram ya yi jawabi ne yayin kaddamar katafaren dakin tiyata a asibitin Airforce da ke jihar Kano.

Ruwan wuta: Gwamnati ta sayi jiragen yaki 30, masu saukar angulu 6 domin yakan Boko Haram
Ruwan wuta: Gwamnati ta sayi jiragen yaki 30, masu saukar angulu 6 domin yakan Boko Haram
Asali: Depositphotos

Ya ce kasar Amurka da Italiya suna taimakawa Najeriya da makamai kare dangi domin yakan Boko Haram da sauran yan baranda a Najeriya.

KU KARANTA: Anyi batakashi tsakanin Soji da yan Boko Haram a Jakana, jihar Borno

A cewarsa, “Gwamnatin shugaba Buhari tayi kokari matuka wajen kawo sauyi hukumar sojin saman Najeriya. A shekaru uku da rabin da suka gabata, gwamnatin tarayya ta sayi sabbin jirage 18.”

“Muna sa ran samun wasu sabbi 12 daga kasar Amurka. Bugu da kari, mun sa ran samun sabbin jirage masu saukar angulu shida daga kasar Italiya.”

“Saboda haka, bisa ga abinda muke samu na gudunmuwa, dukkan hafsoshi da jami’an hukumar sojin sama basu da wani dalili na rashin kokarin kare Najeriya.”

Yayin gabatar da tiyatan, Air Marshal Abba ya ce an gina asibitin ne domin amfanin hafsoshin hukumar da iyalansu. Kana, ya umurci kwamandan asibitin ya tabbatar da cewa masu farar hula.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel