APC za ta dauki kwakkwaran mataki kan Amosun da Okorocha da zaran Buhari ya amince

APC za ta dauki kwakkwaran mataki kan Amosun da Okorocha da zaran Buhari ya amince

- Shuwagabannin jam'iyyar APC sun sha alwashin daukar kwararan matakai kan Gwamna Amosun da takwaransa Okorocha kan yunkurin yiwa jam'iyyar tawaye

- Haka zalika jam'iyyar APC ta fara sa ido kan wasu ministoci guda biyu, Shittu da Dalung, da ma Darakta Janar na muryar Nigeria VON, Mr Osita Okechukwu

- Shuwagabannin jam'iyyar sun ce a yanzu suna jiran umurnin Buhari ne kawai don zartas da wannan hukunci kan masu adawa a hukuncin jam'iyyar

Shuwagabannin jam'iyyar APC na kasa sun kammala yanke shawara kan irin kwararan matakan da zasu dauka kan Gwamna Ibikunle Amosun da takwaransa Rochas Okorocha don ja masu layi kan ci gaba da yin kutse ga ra'ayin jam'iyyar a zabukan gwamnonin jihohin Ogunda Imo.

Duk da cewa, gwamnonin guda biyu sun sha alwashin kin goyon bayan duk wani dan takarar gwamna da jam'iyyar APC da ba tuta a jihohinsu, jaridar Vanguard, a ranar Asabar, ta ruwaito cewa jam'iyyar ta fara sa ido kan wasu ministoci guda biyu, Adebayo Shittu da Solomon Dalung, da ma Darakta Janar na muryar Nigeria VON, Mr Osita Okechukwu.

Amosun da Okorocha sun harzuka ne tun bayan hukuncin shuwagabannin jam'iyyar na kasa na bada takarar kujerorinsu ga wasu mutane da ba su ne suka gabatar ba. Wannan ne dalilin da ya sa gwamnonin biyu suka sha alwashin goyon bayan 'yan takararsu a kowacce jam'iyya suka koma, amma a hannu daya kuma za su ci gaba da goyon bayan tazarcen shugaban kasa Buhari, akan abunda suka kira, namijin kokarin Buharin ne ya ja hakan.

KARANTA WANNAN: 2019: PDP ta yi watsi da Kashamu, ta mika tuta ga 'yan takarar gwamnonin jihohi 3

APC za ta dauki kwakkwaran mataki kan Amosun da Okorocha da zaran Buhari ya amince
APC za ta dauki kwakkwaran mataki kan Amosun da Okorocha da zaran Buhari ya amince
Asali: UGC

Gwamna Amosun a kokarinsa na ganin dan takarar da yake so ya gaje shi, Rep. Sdekule Akinlade ya samu nasara, ya yi wata ganawar sirri da shuwagabannin hukumar tuntuba kan yiwa jam'iyya tawaye IPAC, reshen jihar, don tabbatar da goyon bayansa ga Akinlade.

A bangaren Okorocha kuwa, ya sha alwashin ganin cewa surukinsa, Uche Nwosu ya gaje shi, tare da kuma shan alwashin dakatar da dan takarar APC, Sanata Hope Uzodinma daga gadon kujerarsa ta kowanne hali.

Sai dai ita suma shuwagabannin jam'iyyar APC na kasa, wadanda sam basu ji dadin wadannan matakai na gwamnonin ba, sun tabbatar a cewa jam'iyyar na sane da take takensu na yiwa jam'iyyar tawaye, kuma zasu dauki kwararan matakai akansu.

"Tuni muka yanke shawara kan irin kwararan matakan da zamu dauka akan duk wani mamba jam'iyyar da baya goyon bayan 'yan takarar da jam'iyyar ta gabatar, wanda kuma zamu dauki hakan a matsayin yiwa jam'iyyar twaye." wani daga cikin shuwagabannin jam'iyyar ya shaida hakan ga jaridar Vanguard.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Asali: Legit.ng

Online view pixel