2019: PDP ta yi watsi da Kashamu, ta mika tuta ga 'yan takarar gwamnonin jihohi 3

2019: PDP ta yi watsi da Kashamu, ta mika tuta ga 'yan takarar gwamnonin jihohi 3

- PDP ta gabatar da tutar takara ga 'yan takarar gwamnonin jihohi uku da suka hada da Legas, Oyo da Ogun, domin fuskantar babban zaben 2019

- Uche Secondus, ya ce wadanda suke son yin fito na fito da jam'iyyar da kuma 'yan takararta daga shiyyar Kudu maso Yamma, to su shirya da kyau

- Buruji Kashamu, wanda aka kora daga PDP kwata kwata, ya zama dan takarar gwamnan Ogun karkashin PDP a wani taro da tsagin jam'iyyar ya gudanar

A ranar Juma'ar nan ne shuwagabannin jam'iyyar PDP, a Abuja suka gabatar da tutar takara ga 'yan takarar gwamnonin jihohi uku da suka hada da Legas, Oyo da Ogun, domin fuskantar babban zaben 2019.

Yan takarar sune Ladi Adebutu daga Ogun, Seyi Makinde daga Oyo da kuma Jimi Agbaje daga jihar Legas, wanda ya samu wakilcin Oluwayemisi Busari.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Uche Secondus, a yayin mika tutar jam'iyyar ga 'yan takarar, ya ce wadanda suke son yin fito na fito da jam'iyyar da kuma 'yan takararta daga shiyyar Kudu maso Yamma, to su shirya da kyau.

KARANTA WANNAN: Babachir Lawal ya karyata jawabin Amina Mohammed kan alakanta shi da aikata laifi

2019: PDP ta yi watsi da Kashamu, ta mika tuta ga 'yan takarar gwamnonin jihohi 3
2019: PDP ta yi watsi da Kashamu, ta mika tuta ga 'yan takarar gwamnonin jihohi 3
Asali: UGC

Mr Secondus ya bugi kirji da cewar jam'iyyar PDP ce zata samu nasara a rikicin da ake yi kan kujerar gwamnan jihar Ogun, wanda aka kai maganar gaban kotu, yana mai cewa Mr Adebutu an zabe shi ne ba tare da wata makarkashiya a zaben fitar da gwani ba.

Buruji Kashamu, wani sanata, ya zama dan takarar gwamnan Ogun karkashin PDP a wani taro da tsagin jam'iyyar ya gudanar. Sai dai gaba daya shuwagabannin tsagin jam'iyyar da Mr Kasahamu, sun samu sanarwar korarsu daga jam'iyyar PDP kwata kwata. Lamarin da ya ja har aka kai maganar kotu kan wanda ya cancanta ya zama dan takarar gwamnan Ogun a jam'iyyar.

Mr Secondus ya ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ita ce ta sa ido kan yadda aka PDP ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta, wanda kuma aka aikawa hukumar da sunayen 'yan takara kamar yadda tsarin dokar zabe ya tanadar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Asali: Legit.ng

Online view pixel