Babachir Lawal ya karyata jawabin Amina Mohammed kan alakanta shi da aikata laifi

Babachir Lawal ya karyata jawabin Amina Mohammed kan alakanta shi da aikata laifi

- Babachir David Lawal, ya nisantar da kansa daga wani jawabi da Amina Mohaned ta yi, wanda yake alakantashi da tonon sililin da tayi kan zargin da ake mata na aikata wani laifi

- Babachir ya yi kira ga al'ummar Nigeria da su yi watsi da wannan jawabi na Amina wanda a cewarsa karya ce tsagoranta kuma ya tuntubi lauyoyinsa don daukar mataki

- Kuma ya ce shi baisan wata kanwar matar shugaban kasa Buhari mai suna Maryatu ba, ko kuma Chicason kamar yadda ita Amina ta ambacesu a cikkn jawabin fallasar kan

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya SGF, Babachir David Lawal, ya nisantar da kansa daga wani jawabin da Amina Mohaned ta yi, wanda yake alakantashi da tonon sililin da tayi kan zargin da ake mata na aikata wani laifi.

Babachir ya yi kira ga al'ummar Nigeria da su yi watsi da wannan jawabi na Amina wanda a cewarsa karya ce tsagoranta kuma ya tuntubi lauyoyinsa, wanda kuma nan bada jimawa ba zai dauki matakin da shari'a ta tanadar ta hanyar lauyoyinsa.

Babachir ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

KARANTA WANNAN: PDP: Bamu dauko sojojin haya don gangamin yakin zabe a Sokoto ba, zallar masoya ne

Babachir Lawal ya karyata jawabin Amina Mohammed kan alakanta shi da aikata laifi
Babachir Lawal ya karyata jawabin Amina Mohammed kan alakanta shi da aikata laifi
Asali: Depositphotos

A cewar sanarwar "Labari ya zo mun kan wani jawabin fallasa kai da wata mata tayi mai suna Amina Mohammed dama wasu sa dama, wadanda hukumar tsaro ta DSS ke tuhumarsu kan aikata wani laifi.

" A cikin jawabin fallasa kan da suka rubuta a gaban hukumar wanda kuna ya watsu a tsakanin jama'a, musamman a kafofin sadarwa na zamani, wadanda ake tuhumar sun yi kokarin alakantani da binciken laifin da ake akansu.

"Ina so in shaidawa al'umma cewa, ita Amina Mohammed da ma duk masu alakantani kan tuhumar da ake masu, sam, bani da masaniya kan wannan laifi da suka aikata wanda har ake tuhumarsu akai.

" Ni bansan wata kanwar matar shugaban kasa Buhari mai suna Maryatu ba, ko kuma Chicason kamar yadda ita Amina ta ambacesu a cikin jawabin fallasar kanta.

"Tuni na tuntubi lauyoyi na, don daukar matakin da shari'a ta tanadar akanta. Da wannan kuma nake bukatar daukacin jama'a da su yi watsi da wannan jawabi nata. Na gode, Allah yayi mana albarka baki daya."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Asali: Legit.ng

Online view pixel