Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)

Mataimakin shugaban, farfesa Yemi Osinbajo, ya garzaya kasuwar Ipata dake jihar Kwara a ranan Juma'a, 7 ga watan Disamba, 2018 domin duba yadda ake biyan yan kasuwa bashin N10,000 na kananan yan kasuwan da gwamnatin shugaba Buhari ta kaddamar.

Osinbajo ya samu kyakkyawan tarba daga wajen mutan birnin Ilori tamkar yakin neman zabe yaje. Ya zagaya wurare daban-daban a cikin jihar domin tattaunawa da yan siyasa, sarakuna, da al'ummar jihar gaba daya.

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)
Source: Facebook

Bayan ziyarar da ya kai kasuwan, mataimakin shugaban kasan ya shiga gidan rediyon Sobi 101.9Fm domin tattauna shirin Tradermoni da gwamnatin keyi a fadin tarayya.

Daga baya ya kai ziyarar ban girma fadar sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Kolapo Sulu Gambari, a fadarsa dake birnin Ilori. Ya tafi tare da dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Abdulrahman Abdulrazaq.

A karshe, ya gana da matasa da masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC na jihar Kwara.

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)
Source: Facebook

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)
Source: Facebook

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)

Idonmu ya waye: Yadda mutan jihar Kwara suka tarbi Osinbajo (Hotuna)
Source: Twitter

Hukumar NAN mai dillacin labarai a Najeriya cewa wasu tsageru sun kawo hatsaniya a cikin Garin Ilorin a Jihar Kwara a daidai lokacin da Jami’an Gwamnati ke shirin raba tallafin nan na TraderMoni jiya da safe.

Mun kawo muku rahoton wasu fitinannun mutane sun hargitsa kasuwar Garin Ilorin a sa’ilin da ake kokarin bada gudumuwa ga masu karamin karfi a cikin kasuwar. Kamar yadda mu ka samu labari, wadannan Matasa su na sanye ne rigunan Atiku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel