Majalisar Dinkin Duniya ta janye ma’aikata daga Rann yayinda Boko Haram suka kai hari sansanin yan gudun hijira

Majalisar Dinkin Duniya ta janye ma’aikata daga Rann yayinda Boko Haram suka kai hari sansanin yan gudun hijira

Sashin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi dukkanin ma’aikatan agaji da ke aiki a yanzu a Rann da su kwashe ma’aikatansu biyo bayan harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai kan sansanin yan gudun hijira a daren jiya.

Fannin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi dukkanin ma’aikatan agaji da ke aiki a yanzu a Rann da su kwashe ma’aikatansu biyo bayan harin da aka kai kan sansanin yan gudun hijira a daren jiya.

Majalisar Dinkin Duniyan ta yi gargadin ne a ranar Juma’a, 7 ga watan Disamba, jaridar DailyTrust ta ruwaito.

Majalisar Dinkin Duniya ta janye ma’aikata daga Rann yayinda Boko Haram suka kai hari sansanin yan gudun hijira
Majalisar Dinkin Duniya ta janye ma’aikata daga Rann yayinda Boko Haram suka kai hari sansanin yan gudun hijira
Asali: Depositphotos

Idan za’a tuna wasu dakunan karban magunguna sun one a harin da sojoji suka dakile a sansanin yan gudun hijiran.

Ga yadda jawabin ya zo: “Sakamakon halin da tsaro ke ciki a Rann, da kuma bayanan da akasamu daga INSO da UNDSS, dan Allah k sani cewa muna shirin canza wa ma’aikata wuri daga Rann zuwa Maiduguri a yau, Juma’a, 7 ga watan Disamba, ga hukumomin da ke da niyan sauya wa ma’aikatans wauri saboda harin toh su aikata hakan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Wani gidan mai kusa da filin jirgin saman Lagas ya kama da wuta

“Kamar yadda muka samu labari, an sanar da sauya wa ma’aikatan agaji 24 wuri daga hukumomin agaji takwas. Kusan dukkanin hukumomin da ma’aikatansu ke kasa an bukaci su aikata hakan.

“UNSS da INSO na kula da lamarin tsaro, sannan duk wani Karin shawara zai biyo baya."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel