Debo ruwan dafa kai: Wani saurayi ya kashe budurwarsa tare da binne gawarta a dakinsa
-Wani saurayi da aka bayyana sunansa da Prince Owabie, ya kashe budurwarsa wacce kuma ke dauke da cikinsa, tare da binne gawarta a cikin dakinsa a garin Fatakwal
- Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar 2 ga watan Disamba, a sha-tale-talen Wimpy, titin Ikweere
- Rundunar 'yan sanda ta ce wanda ake zargin an kaishi zuwa sashin bincike masu aikata laifukan ta'addanci na jihar
Rahotannin da Legit.ng ta samu, na nuni da cewa wani saurayi da aka bayyana sunansa da Prince Owabie, ya kashe budurwarsa wacce kuma ke dauke da cikinsa, tare da binne gawarta a cikin dakinsa a garin Fatakwal.
Owabie, wanda aka fi sani da J-BOY ya tonawa kansa asiri, bayan sanar da abokansa kwanaki biyu da wannan aika aikar da yayi.
Sai dai, cikin rashin sa'a ga J-BOY, abokan nasa suka sanarwa rundunar 'yan sanda ta jihar Rivers wacce kuma ta tura jami'anta suka cafko shi.
KARANTA WANNAN: Mu leka kotu: An garkame wani dan aikin gida bayan satar sarkar N300,000 mallakin matar gida

Asali: Facebook
Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar 2 ga watan Disamba, a sha-tale-talen Wimpy, titin Ikweere.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, DSP Nnamdi Omoni, ya ce wanda ake zargin an kaishi zuwa sashin bincike masu aikata laifukan ta'addanci na jihar.
DSP Nnamdi ya kara da cewa rundunar ta tura jami'anta zuwa wurin da lamarin ya faru don tono gawar.
"Muna da kwararan bayanai kan cewar J-BOY ya haka rami a cikin dakinsa inda ya bunne budurwarsa," a cewarsa.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co
Asali: Legit.ng