Akwai dalilin da ya sa Buhari bai kamata ya sa hannu a dokar zabe ta 2018 ba

Akwai dalilin da ya sa Buhari bai kamata ya sa hannu a dokar zabe ta 2018 ba

- A makon da ya gabata, wasu jam'iyyun siyasa guda 3 suka je babbar kotun gwamnatin tarayyA, Abuja, don bukatar kotun ta dakatar da Buhari daga sa hannu a dokar zaben 2018

- Babban abun daga hankalin shiene yadda NASS ke son tilasta amfani da tsarin zabe ta hanyar na'ura mai kwakwalwa da kuma bayyana sakamako kai tsaye a zaben 2019

- Haka zalika, idan shugaban kasar ya amince da dokar zaben 2018, to ya saba da tsarin kungiyar Africa AUP, na cewar ba a yarda a sake fuska ga dokar da ta shafi zabe ba

Hakika bun takaici ne yadda masu kafa doka a kasar (majalisun tarayya), zasu samar da dokokin da suka saba da tunanin al'umomin da suke wakilta, da kuma hana wadannan mutane 'yancin zabar shuwagabannin da suke muradi a zaben 2019.

Wannan kuwa na cikin bahallatsar da ta mamaye dokar zabe da aka sabuntata a 2018, aka gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu, bayan da majaisun tarayyar suka amince da ita.

A makon da ya gabata, wasu jam'iyyun siyasa guda 3 suka je babbar kotun gwamnatin tarayy, Abuja, don bukatar kotun ta dakatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari daga sa hannu a kan wannan doka. Jam'iyyun siyasar sune: Advanced Peoples Democratic Alliance, (APDA), Allied Peoples Movement, (APM) and Movement for Restoration, da Defence of Democracy, (MRDD).

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Hukumar NYSC zata baiwa INEC matasa 20,000 don zama jami'an zabe

Akwai dalilin da ya sa Buhari bai kamata ya sa hannu a dokar zabe ta 2018 ba

Akwai dalilin da ya sa Buhari bai kamata ya sa hannu a dokar zabe ta 2018 ba
Source: Twitter

Lauyan wadanda suka gabatrwa kotun wannan bukatar, Dapo Otitoju, ya bayyanawa manema labarai cewa sun barwa kotun tambayayoyi biyu don yin nazari akansu.

"Na daya, ko akwai yiyuwar shugaban kasa ya sa hannu akan dokar zaben da aka sabunta a 2018, wacce majalisun tarayya suka gabatar masa, da zummar gudanar da zabukan 2019, a yayin da aka san babu wani isasshen lokaci na bin diddigin abubuwan da dokar ta kunsa.

"Da kuma, ko akwai yiyuwar shugaban kasar ya sa hannu akan dokar zaben wacce aka sabunta a 2018, a dai dai wannan lokaci, ba tare da ta sa shakku a zuciyar shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC ba, na gudanar da sahihin zabe a 2019."

DUBA WANNAN: Majalisar wakilai ta janye kudurin dokar hana 'yayan jami'an gwamnati karatu a kasashen waje

Babban abun daga hankalin shiene yadda NASS ke son tilasta amfani da tsarin zabe ta hanyar na'ura mai kwakwalwa da kuma bayyana sakamako kai tsaye a zaben 2019. Wannan kuwa, babu yadda za'a iya cimma tsarin kafin zaben, sa hannu a dokar zai sanya zaben cikin wani mummunan hali.

Sai kuma bangaren da yafi sanya tunani, shine rashin sahihanci a dokar da aka sabunta wacce ba a gane inda ta dosa ba. Abun dubawar shine, babu yadda za'ayi a aiwatar da komai na dokar kafin zabe, wanda hakan zai iya haddasa rikici a zaben wanda tuni aka kusa kammala shirye shiryensa.

LEKA WANNAN: Karka biyewa masu kokarin hanaka sa hannu a kudurin dokar zabe - Saraki ya shawarci Buhari

Shin NASS ba zata iya bari har sai bayan zaben 2019 ta gabatar da dokar zaben ba? Ko dai wasu na son amfani da sabuwar dokar don kawo rudani a yayin zaben? La'akari da cewar idan aka amince da dokar, to hakan zai lalata duk wasu tanade-tanade da aka kammala na gudanar da zaben a watanni 2 masu zuwa.

Haka zalika, idan shugaban kasar ya amince da dokar zaben 2018, to ya saba da tsarin kungiyar Africa AUP, na cewar ba a yarda a sake fuska ko bullo da sabuwar doka da ta shafi zabe ba, a watanni 3 gabanin zaben, a kowanne hali.

Wannan rubutun, RA'AYIN Obi ne daga Abuja, wanda aka wallafa a shafin jaridar Daily Trust, a ranar 06 ga watan Disamba, 2018.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel