2019: Karshen mulkin Shugaba Buhari ya karaso - Inji Jam'iyyar PDP

2019: Karshen mulkin Shugaba Buhari ya karaso - Inji Jam'iyyar PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jiya Laraba, 5 ga watan Disamba sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya fara tattara komatsan sa daga fadar shugaban kasa a wajen gangamin kamfen din ta a Ilorin, jihar Kwara.

Darakta janar na kungiyar kamfen din Atiku kuma shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki ya ce gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta gaza sosai wajen shugabanci.

2019: Karshen mulkin Shugaba Buhari ya karaso - Inji Jam'iyyar PDP

2019: Karshen mulkin Shugaba Buhari ya karaso - Inji Jam'iyyar PDP
Source: Facebook

Ya bukaci yan Najeiya da su kora Buhari da APC a zabe mai zuwa, inda ya bayyana cewa APC ta gaza cika dukka alkawaran da ta dauka a zaben 2015.

KU KARANTA KUMA: Obasanjo na gayyatar fushin Allah - Oshiomhole

Atiku yayi korafin cewa kasar ta lalace a karkashin APC, do haka akwai bukatar samar da mafita da zai daidaita lamura.

Atiku yayi zargin cewa shirin APC na siyan katunan zabe daga mutane wata hanya ce ta zambar zabe, amma ya bukaci yan Najeriya da kada su aminta da wannan shiri saboda makomar rayuwarsu da ta yayansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel