Karka biyewa masu kokarin hanaka sa hannu a kudurin dokar zabe - Saraki ya shawarci Buhari

Karka biyewa masu kokarin hanaka sa hannu a kudurin dokar zabe - Saraki ya shawarci Buhari

- Bukola Saraki, ya shawarci Buhari da ya toshe kunnuwansa daga hudubar 'yan kazagi, da ke kokarin matsa masa lamba kan kar ya sanya hannu a kudurin dokar zaben 2018

- Ya bukaci shugaban kasar da ya tashi tsaye haikan kan irin wadannan mutane, da kuma gaggauta sa hannu kan kudurin dokar don tabbatar da ita cikakkiyar doka

- A cewarsa Saraki dokar zaben zata magance matsalolin da za a iya fuskanta a zaben, tare da tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe wanda babu magudi a ciki

Shugaban majalisar datiijai na kasa, Dr Abubakar Bukola Saraki, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya toshe kunnuwansa daga hudubar 'yan kazagi, da ke kokarin yiwa demokaradiyyar kasar karan tsaye, masu matsa masa lamba kan kar ya sanya hannu a dokar zaben 2018.

Saraki a cikin wata sanarwa a Ilorin a ranar Laraba daga hannun mai bashi shawara kan watsa labarai, Yusuph Olaniyonu, ya buykaci shugaban kasar da ya tashi tsaye haikan kan irin wadannan mutane, da kuma gaggauta sa hannu kan kudurin dokar don tabbatar da ita cikakkiyar doka.

KARANTA WANNAN: Ga mai sha'awa: Canada tana bukatar ma'aikata 430,000

Saraki ya yi nuni da cewa, yana ta samun kiraye kiraye daga mambobin majalisun tarayya wadanda ke nuna damuwarsu kan tsaikon da ake samu na kin sa hannu kan kudurin dokar zaben, duba da cewa wa'adin wata daya da doka ta tanadarwa shugaban kasa ya sa hannu akan kudurin doka har ya wuce kwanaki da suka shude.

Karka biyewa masu kokarin hanaka sa hannu a kudurin dokar zabe - Saraki ya shawarci Buhari
Karka biyewa masu kokarin hanaka sa hannu a kudurin dokar zabe - Saraki ya shawarci Buhari
Asali: UGC

Ya kara da cewa da yawa daga cikin 'yan majalisar da suka tuntube shi, sun damu kwarai kan yadda wasu mutane da ake ganin suna shugabantar jam'iyyun siyasa a kasar, sun je babbar kotun gwamnatin tarayya don dakatar da shugaban kasar daga sa hannu kan kudurin dokar.

Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nisantar da kansa daga irin wadannan marasa kishin demokaradiyyar kasar, tare da sa hannu kan kudurin dokar, wanda a cewarsa ya magance matsalolin da za a iya fuskanta a zaben, tare da tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe wanda babu magudi ko tashin hankali a ciki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel