Oby Ezekwesili ta ce ko kadan gwamnatinta ba zata kyamaci 'yan luwadi da 'yan madigo ba

Oby Ezekwesili ta ce ko kadan gwamnatinta ba zata kyamaci 'yan luwadi da 'yan madigo ba

Yar takarar shugabar kasar Nigeria karkashin jam'iyar ACPN, Obiageli Ezekwesili ta tabbatar da cewa gwamnatinta zata yi adalci ko kwanne irin mutum ba tare da duba dabi'arsa ba, wandanda suka hada da 'yan luwadi da 'yan madigo (LGBT).

Ta bayyana hakan ne a lokacin da aka tambayeta, a wata tattaunawa da Bisi Alimi tayi da ita a kasar Landan, kan cewar ko zata sakarwa 'yan madigo da 'yan luwadi mara idan ta zama shugabar kasa.

KARANTA WANNAN: Yau ake gudanar da jana'izar tsohon shugaban amurka HW Bush

Oby Ezekwesili ta ce ko kadan gwamnatinta ba zata kyamaci 'yan luwadi da 'yan madigo ba

Oby Ezekwesili ta ce ko kadan gwamnatinta ba zata kyamaci 'yan luwadi da 'yan madigo ba
Source: Twitter

Ta ce, "Idan har za a yi adalci ga kowa, to babu dalilin nuna tsangwama ga wasu bangare na mutane. Ko kadan ba zan damu da yardar ka ba, ko wata hanya da ka zabi binta, kowa nada ra'ayinsa, kuma kowa na da 'yancin bin wannan ra'ayin.

"Na yarda da tafiyar da mutane kan gaskiya da adalci, don haka al'umar LGBT zasu skata su wala a gwamnatina ba tare da wani shakku ba. Kuma rashin nuna kyama ga wani bangare na al'uma na daga cikin tsarin gwamnatina idan har na zama shugabar kasa."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel